Bello Turji Ya Firgita a cikin Daji, Yana Gudun Neman Tsira Zuwa Wurare
- Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dan ta'adda, Bello Turji, wanda ake nema ruwa a jallo, na fuskantar matsin lamba mai tsanani
- Babban kwamandan rundunar hadin gwiwa ya ce bayanan sirri na nuna cewa Turji da mutanensa na ta kaura lokaci zuwa lokaci saboda firgita
- Sojoji sun kuma yi watsi da rade-radin cewa Turji na da iko da wasu kananan hukumomi, suna masu kiran hakan farfagandar ‘yan ta’adda
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - Rundunar sojin Najeriya ta ce jagoran ‘yan bindiga da ake nema, Bello Turji, na cikin yanayin firgici da rudani bayan tsananta hare-haren soji a kan shi da sauran ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma.
Wannan bayani ya fito ne daga babban kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Operation Fansan Yamma, Manjo Janar Warrah Idris, yayin wata ziyara da ‘yan jaridu masu bibiyar harkokin tsaro suka kai filin ayyukan soji a jihar Zamfara.

Source: UGC
Tribune ta wallafa cewa Janar Idris ya ce duk da cewa Turji bai kamu a hannu ba har yanzu, rundunar soji na ci gaba da matsa masa lamba.
Bello Turji ya firgita a cikin daji
Manjo Janar Warrah Idris ya bayyana cewa rahotannin bayanan sirri na baya-bayan nan sun nuna cewa Bello Turji da sauran ‘yan bindiga na cikin matsanancin firgici sakamakon tsauraran matakan soji.
A cewarsa:
“Dangane da sahihan bayanan sirri da muke da su a yanzu, Bello Turji da sauran mutanensa na cikin rudani da firgici saboda karfin ayyukan da muke gudanarwa. Suna canza wurin zama duk bayan wasu awanni ko kwanaki.”
Ya kara da cewa irin wannan yanayi na nuna cewa ayyukan soji na ci gaba da yin tasiri a kansu, duk da cewa suna kokarin kauce wa cafkewa.
Turji bai kwace ikon karamar hukuma ba
Babban kwamandan rundunar hadin gwiwar ya yi watsi da ikirarin da ke yawo cewa Bello Turji na iko da wasu kananan hukumomi ko kauyuka.

Kara karanta wannan
An fitar da sunayen mutane 177 da 'yan bindiga suka sace suna tsakiyar ibada a Kaduna
Ya bayyana wadannan ikirari a matsayin farfagandar ‘yan ta’adda, yana mai cewa mutum da ba shi da tabbataccen matsuguni ba zai iya mallakar wani yanki ba.
A cewarsa:
“Ta yaya wanda ba shi da wurin zama na dindindin zai ce yana iko da wata karamar hukuma? Ina kalubalantar Bello Turji ya fito ya ambaci ko karamar hukuma guda daya da yake ikirarin yana iko da ita.”

Source: Facebook
Ana bincike kan sauran ‘yan bindiga
Janar Idris ya kara da cewa rundunar soji na bibiyar wasu fitattun shugabannin ‘yan bindiga da suka hada da Gwaska, Ado Aliero da Dogo Gide a karkashin rundunar Operation Fansan Yamma.
Ya ce ana bin diddigin wadannan mutane ne ta hanyar dukkan hanyoyin bayanan sirri da rundunar ke da su, tare da tsare-tsaren aiki na soja masu tsauri.
Rahoton da Daily Post ta wallafa ya nuna cewa ya ce idan komai ya tafi daidai, Bello Turji da irinsa za su zama tarihi a Arewa maso Yamma.
Sojoji sun gano rumbun Boko Haram
A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar sojin Najeriya ta kai wasu munanan hare-hare kan 'yan ta'addan Boko Harama a Borno.
Rahotannin da dakarun Najeriya suka fitar sun nuna cewa sun yi nasarar gano wani rumbun ajiya da 'yan ta'addan ke amfani da shi.
Bayan gano rumbun ajiyar da ke karkashin kasa, sojoji sun kashe wasu 'yan ta'addan tare da kwato wata mota da suke amfani da ita.
Asali: Legit.ng

