Gwamna Uba Sani Ya Gano Cibiyar 'Yan Bindiga da Ayyukan Ta'addanci a Najeriya

Gwamna Uba Sani Ya Gano Cibiyar 'Yan Bindiga da Ayyukan Ta'addanci a Najeriya

  • Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya koka kan zargin garin Rijana da taimaka wa ayyukan ta'addanci a Najeriya
  • Sanata Uba Sani ya fito fili ya ayyana garin, wanda ke kan titin Kaduna zuwa Abuja, a matsayin cibiyar 'yan bindiga da ayyukan ta'addanci
  • Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya taba barazanar tada garin kan zargin taimakawa yan ta'adda da ke addabar jama'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Gwamnan Jihar Kaduna, Malam ba Sani ya gano cibiyar rashin tsaro da ayyukan ta'addanci a Najeriya.

Sanata Uba Sani ya bayyana garin Rijana da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a Karamar Hukumar Kachia ta jihar, a matsayin cibiyar rashin tsaro da ayyukan ta'addanci a kasar nan.

Malam Uba Sani.
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani yana jawabi a taro Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

El-Rufa'i ya taba daukar zafi kan Rijana

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta tabo batun kisan matar aure da 'ya'yanta a Kano

Jaridar Leadership ta tattaro cewa a baya, tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya taba bayar da shawarar tashin jama'ar Rijana daga garin gaba daya.

A lokacin mulkinsa, Malam El-Rufai ya ce tada garin Rijana shi ne mafita saboda zargin cewa garin na boye miyagun mutane da masu aikata manyan laifuffuka na ta'addanci.

Wannan kalamai da tsohon gwamnan ya yi sun ja hankali daga bangarori daban-daban na kasar nan, inda wasu musamman 'yan adawa a wancan lokaci, suka rika sukarsa.

Gwamna Uba Sani ya koka kan Rijana

A halin yanzu, Gwamna Uba Sani ya koka kan abubuwan da ke faruwa a garin, inda ya ayyana Rijana a matsayin matattarar 'yan bindiga da ayyyukan ta'addanci a Najeriya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai kauyen Kurmin Wali da ke Karamar Hukumar Kajuru, inda ake zargin 'yan bindiga sun sace mutane 177 a coci uku.

Maharan sun farmaki cocin ne a ranar Lahadi da ta gabata, lokacin da mutane suka hallara domin ibadar karshen mako kamar yadda suka saba.

Kara karanta wannan

'Dalilin da zai sanya Peter Obi ya fice daga jam'iyyar ADC kafin zaben 2027'

Alkawarin da Uba Sani ya dauka

Uba Sani ya tabbatar wa al'ummar yankin cewa mutanen da aka sace za su dawo gida lafiya, inda ya kuma yi kira ga Gwamnatinn Tarayya da ta kafa sansanin soja a Kurmin Wali, duba da kusancinsa da garin Rijana.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, tun farko gwamnatin Kaduna da Rundunar 'Yan Sandan Jihar sun musanta faruwar wannan hari na garkuwa da mutane.

Gwamna Uba Sani.
Gwamna Uba Sani a fadar gwamnatin jihar Kaduna Hoto: Uba Sani
Source: Twitter

Amma daga bisani rundunar yan sandan Najeriya ta tabbatar da kai harin, inda ta ce sufetan yan sanda na kasa ya tura dakaru na musamman domin ceto wadanda aka sace.

A yau Laraba kuma Gwamna Uba Sani ya je har garin domin jajantawa al'umma tare da tabbatar musu da cewa za a ceto yan uwansu cikin koshin lafiya.

An fitar da sunayen wadanda aka sace a coci

A wani labarin, kun ji cewa an fitar da sunayen mutanen da aka sace yayin wani hari da 'yan bindiga suka kai wa coci guda uku a Karamar Hukumar Kajuru da ke Jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Sheikh Daurawa ya je ta'aziyya ga magaidancin da aka kashewa iyali a Kano ya yi masa nasiha

‘Yan bindiga sun kutsa kauyen Kurmin Wali a ranar Lahadi, inda suka rika bi daga coci daya zuwa wani, suka sace akalla masu ibada 177.

Shugaban Kungiyar Raya Karkara ta Adara (ADA), wata kungiya da ke wakiltar kabilar Adara a Karamar Hukumar Kajuru, ya fitar da jerin sunayen mutanen da aka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262