Atiku Ya Yi Magana kan Sace Masu Ibada a Kaduna, Ya Fadi Kuskuren Gwamnati

Atiku Ya Yi Magana kan Sace Masu Ibada a Kaduna, Ya Fadi Kuskuren Gwamnati

  • Ana ci gaba da jimamin harin da 'yan bindiga suka kai a jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da masu ibada a coci
  • Tsohon Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya fito ya nuna alhininsa kan sace mutanen da 'yan bindiga suka yi
  • Atiku Abubakar ya nuna cewa ya kamata gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta dauko alhakin kasa cika alkawuran da ta dauka kan matsalar rashin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar suka kan sababbin hare-haren ‘yan bindiga a Kajuru, jihar Kaduna.

Atiku ya yi gargadin cewa yarjejeniyoyin sulhu da masu laifi sau da yawa kan fifita ‘yan bindiga fiye da mutanen da ake cutarwa.

Atiku ya yi Allah wadai da harin 'yan bindiga a Kaduna
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar Hoto: @Atiku
Source: Twitter

Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya fitar a shafinsa na X a ranar Laraba, 21 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

An fitar da sunayen mutane 177 da 'yan bindiga suka sace suna tsakiyar ibada a Kaduna

Ya jaddada cewa ya kamata tatttaunawar da gwamnati ke yi da ‘yan bindiga ta mayar da hankali kan kare al’umma da mutunta hakkokinsu, ba wai bai wa masu laifi fifiko ba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta kasa, CSP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar a ranar Talata cewa ‘yan bindiga sun sace wasu masu ibada a yayin ibadar coci a Kajuru ranar Lahadi.

Me Atiku ya ce kan harin Kaduna?

Da yake mayar da martani kan labarin, Atiku ya nuna damuwa matuka kan karuwar karfin gwiwar ‘yan bindiga, inda ya ce suna ci gaba da kai hare-hare kan al’umma ba tare da tsoron hukunci ba.

Ya ce abin tayar da hankali ne ganin cewa, duk da ikirarin da wasu jihohi ke yi na samun ci gaba ta hanyar yarjejeniyar sulhu, har yanzu ‘yan bindiga na ci gaba da sace mutane da kai hare-hare.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce:

“Yana da wahala a samu tsoratarwa da hana aikata laifi a yanayin da gwamnonin jihohi ke durkusawa suna rokon ‘yan bindiga da sunan yarjejeniyar sulhu.”

Atiku ya soki yadda ake sulhu da 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Makwabtan Fatima da aka kashe da yaranta 6 a Kano sun fusata rundunar 'yan sanda

Ya kara da cewa, duk da ba ya adawa da tattaunawa domin kawo karshen tashin hankali, ba zai amince da yanayin da ‘yan bindiga ke tsara sharuddan sulhu bisa yadda suke so ba.

“Irin wadannan yarjejeniyoyi a kullum suna amfanar da ‘yan bindiga fiye da wadanda suka zalunta, kuma sau da dama sun rika yaudarar wakilan gwamnati da ke shiga tattaunawar."

- Atiku Abubakar

Atiku ya soki yadda gwamnati ke sulhu da 'yan bindiga
Atiku Abubakar na jawabi a wajen wani taro Hoto: Mustapha Sule Lamido
Source: Facebook

Atiku ya ba gwamnatin Najeriya shawara

Atiku ya kuma shawarci gwamnati da kada ta jira sai ‘yan bindiga sun kai hari kafin ta dauki mataki.

“’Yan Najeriya sun daina jin dadin kalaman Allah-wadai daga gwamnati. Abin da suke so shi ne su gani a kasa, ba surutai ba."
"Abubuwan da suka faru sun nuna cewa da kalamai kadai za su hana ‘yan bindiga, da tuni an kawo karshen wannan matsala.”

- Atiku Abubakar

Ya jaddada cewa ya kamata gwamnatin APC karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dauki alhakin rashin cika alkawurran da ta dauka a yakin neman zabe na magance matsalar tsaro a fadin kasar nan.

'Yan sanda sun musanta sace mutane a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa Kwamishinan 'yan sanda jihar Kaduna, ya musanta batun sace masu ibada a karamar hukumar Kajuru.

Kara karanta wannan

Yadda tubabbun 'yan bindiga suka taimaka aka kashe tsageru 50 a Katsina

Alhaji Muhammad Rabiu ya bayyana rahotannin da ke cewa an sace masu ibada 163 a karamar hukumar Kajuru a matsayin wadanda babu kamshin gaskiya a cikinsu.

Kwamishinan ’yan sandan ya kalubalanci duk wanda ke yin wannan ikirari da ya fito ya bayyana sunayen waɗanda ake zargin an sace tare da bayar da cikakkun bayanansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng