Yan Bindiga Sun Yi wa Shugaban Karamar Hukuma, Jami’an Tsaro Kwanton Bauna a Zamfara
- Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kai hari kan tawagar tsaro tare da Shugaban Karamar Hukumar Tsafe a jihar Zamfara
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun kai harin ne a hanyar Kunchin Kalgo–Danjibga a Zamfara da ke fama da matsalolin tsaro
- Harin ya faru ne yayin da tawagar ke kan hanyarta ta kai wasu ’yan ƙauye da aka kuɓutar daga hannun masu garkuwa zuwa Danjibga
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Rundunar ’yan sanda ta bayyana cewa wasu ’yan bindiga da ake zargi sun kai hari a jihar Zamfara a ranar 20 ga watan Janairun 2026 a jihar Zamfara.
Harin ya faru ne a kan hanyar Kunchin Kalgo zuwa Danjibga da ke cikin karamar hukumar Tsafe, inda tawagar ke tafiya tare da Shugaban Karamar Hukumar Tsafe.

Source: Original
Majiyoyi sun shaida wa Zagazola Makama cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 7:30 na yamma a ranar 20 ga watan Janairun 2026.
Yan bindiga sun sace shanu 500 a Zamfara
Wannan na zuwa ne kwanaki hudu kacal bayan mahara sun kai wani hari a jihar inda suka sace shanu da dama.
'Yan bindiga dauke da mugayen makamai sun kai farmaki babbar kasuwar dabbobi a karamar hukumar Kaura Namoda, jihar Zamfara.
Rahoto ya nuna cewa maharan sun kwace tare da yin awon gaba da shanu fiye da 500 a harin, amma an yi nasarar dawo da 60.
Shugaban kungiyar makiyaya (MACBAN) reshen jihar Zamfara, Aminu Garba ya ce wannan ba shi ne karo na farko da 'yan bindiga suka farmake su ba.

Source: Facebook
Yadda harin yan bindiga ya faru a Zamfara
Rahotanni sun nuna cewa tawagar tsaro na kan hanyarta ne zuwa Danjibga domin haɗa wasu mazauna yankin Keta da aka kuɓutar daga hannun masu garkuwa da mutane.
Majiyoyin sun ce ’yan bindigar sun shirya kwanton ɓauna a hanyar, lamarin da ke nuna sun riga sun san shirin tawagar tsaron.
Bayan kai harin, an ce Shugaban Karamar Hukumar Tsafe da mutanen da ke tare da shi sun makale a Danjibga.
Har ila yau, ana fargabar cewa wasu mutane sun faɗa hannun ’yan bindigar, yayin da ake zargin an ƙona wasu motoci.
Majiyoyin sun ƙara da cewa an tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin domin kuɓutar da mutanen da suka makale da kuma dawo da zaman lafiya.
A halin yanzu dai, jami’an tsaro na ci gaba da bincike domin gano cikakken abin da ya faru, tare da ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin.
Bam ya tarwatse da matafiya a Zamfara
A baya, mun ba ku labarin cewa wani abin fashewa da ake zargin bam ne da 'yan bindiga suka dasa ya tashi da matafiya a jihar Zamfara.
Lamarin ya auku ne lokacin da mutanen suke tsaka da tafiya a kan hanya, kwatsam kawai sai suka taka bam din da aka dasa.
Fashewar bam din ta jawo jami'an tsaro sun takaita zirga-zirga a kan hanyar yayin da suke ci gaba da kokarin dakile duk wata barazana.
Asali: Legit.ng

