Yan Sanda Sun Canja Zance kan Zargin Sace Masu Ibada 160 a Kaduna

Yan Sanda Sun Canja Zance kan Zargin Sace Masu Ibada 160 a Kaduna

  • Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da sace kiristoci 100 a Kurmin Wali, Kajuru, Kaduna bayan sun karyata labarin da ya bulla da farko a kan lamarin
  • Bayan samun bullar labarin cewa an sace masu ibada, rundunar yan sandan Kaduna ta fitar da sanarwar da wasu suka fassara a matsayin karyata harin
  • Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya ba da umarnin tura ƙwararrun jami’ai da kayan leƙen asiri yankin da niyyar ceto su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta tabbatar da sace kiristoci sama da 100 a Kurmin Wali, a ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Rundunar ta tabbatar da garkuwa da bayin Allah masu tarin yawa bayan da ta karyata cewa an dauke mutanen a wuraren ibadarsu.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano babban rumbun ajiyar kayan Boko Haram a karkashin kasa

Yan sanda sun tabbatar da harin Kaduna
Sufeton yan sanda, Kayode Egbetokun tare da wasu jami'an tsaro Hoto: Nigerian Police Force
Source: Facebook

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Talata, kakakin rundunar ‘yan sanda ta ƙasa, CSP Benjamin Hundeyin ya yi karin haske a kan harin.

Kaduna: Yan sanda sun yi bayanin sace kiristoci

The Cable ta wallafa cewa rundunar yan sanda ta ce an jirkita kalaman da Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kaduna, kuma ba a fahimta dai-dai ba.

Rundunar ta jaddada cewa maganganun ba musanta aukuwar lamarin ba, illa an bayar da amsar da ta dace a lokacin da ake jiran cikakken bayani daga jami’an da ke bakin aiki.

Sanarwar ta ƙara da cewa binciken da sassan ayyukan musamman da na bayanan sirri suka gudanar daga bisani ya tabbatar da cewa an sace mutane da dama.

Ana kokarin ceto masu ibada da aka sace a Kaduna
Gwaman Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani Hoto: Sen Uba Sani
Source: Facebook

Bayan tabbatar da aukuwar lamarin, rundunar ‘yan sanda ta ce an kaddamar da ayyukan tsaro tare da sauran hukumomin tsaro, inda aka mai da hankali kan ceto waɗanda aka sace.

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin Najeriya sun shirya yin bore? An ji gaskiyar zance

Haka kuma jami'an suna kokarin shawo kan matsalar tsaro da kuma dawo da kwanciyar hankali a yankin da aka kwashe jama'a.

Ana aikin ceto mutanen Kaduna - Yan sanda

A cewar sanarwar, Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin tura manyan kayan aiki na tsaro da na leƙen asiri zuwa Kajuru da al’ummomin da ke kewaye da yankin.

Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da kafafen yaɗa labarai da su yi hakuri da kara nutsuwa, tare da dogaro da sahihan bayanai daga hanyoyin hukuma wajen samun labarai.

Sanarwar ta ƙare da cewa rundunar ‘yan sanda ta jajirce ƙwarai wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa, kuma za ta ci gaba da sanar da jama’a duk wani sabon ci gaba da ya taso kan lamarin.

An hallaka Malami a Kaduna

A baya, mun wallafa cewa wani fitaccen malamin addinin Musulunci, Alaramma Malam Bello Abubakar, wanda ya shahara wajen tafsirin Alƙur’ani a masallacin JIBWIS, ya rasa ransa a hannun ‘yan bindiga a jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe malamin ne a unguwa Layin Dan’auta da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari, bayan da ya yi arangama da ‘yan bindiga a yankin, lamarin da ya jawo tashin hankali a yankin.

Kara karanta wannan

Abba, Barau da hukumomi 2 da suka yi alkawarin nema wa Fatima da yaranta 6 adalci

Rahotanni sun nuna cewa an hallaka malamin nan take, ba tare da samun damar tsira ba, lamarin da ya ƙara tayar da hankula a Birnin Gwari, yankin da ya dade yana fama da matsalolin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng