Jami'an DSS Sun Mika Bukata ga Kotu game da Garkame Abubakar Malami SAN
- Rahotanni sun bayyana cewa hukumar DSS na neman umarnin kotu domin tsawaita tsare tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami SAN
- Jami'an DSS sun sake cafke Abubakar Malami mintuna kadan bayan ya kammala sharuɗɗan beli daga gidan yari na Kuje bayan tsare shi
- Ana bincikensa kan zargin boye dukiya, da kuma jerin masu daukar nauyin ta’addanci na UAE bayan jami'an sun samu makamai a gidansa da ke Kebbi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), na iya kwashe lokaci mai tsawo a hannun Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS).
Majiyoyin tsaro da dama sun bayyana cewa DSS na shirin neman umarnin kotu domin ci gaba da tsare Malami har sai an kammala binciken da ake yi a kansa.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa sun ce yanayin binciken na da sarkakiya kuma yana da matuƙar muhimmanci, abin da ka iya daukar watanni kafin a kammala.
Abubakar Malami ya shiga hannun DSS
The Nation ta wallafa cewa sabon halin da Malami ya tsinci kansa ya fara ne a ranar Litinin, 19 ga watan Janairu, 2026 lokacin da jami’an DSS suka sake cafke shi bayan ya fito daga kotu.
An cafke shi ne ‘yan mintuna kacal bayan fitowarsa daga gidan yarin, inda ya shafe makonni tun daga farkon Disamba bisa zargin da Hukumar EFCC ta shigar a kansa.
Majiyoyin tsaro sun ce DSS na neman umarnin kotu ne saboda tsananin sarkakiya da sirrin binciken da ake gudanarwa, wanda ake sa ran zai dauki dogon lokaci.
Tun da farko, EFCC ta cafke Malami ne bisa zargin hada baki da matarsa, Asabe, da dansu wajen boye haramtattun kudi ayyuka da darajarsu ta kai kusan Naira biliyan 8.7.

Kara karanta wannan
Abba, Barau da hukumomi 2 da suka yi alkawarin nema wa Fatima da yaranta 6 adalci
Zargin da EFCC ke yi wa Malami
EFCC ta ce ana yi wa Abubakar Malami SAN zargin amfani da kamfanoni da dama, asusun banki, da kuma saye-sayen kadarorin alfarma a Abuja da wasu sassan kasar nan.
A ranar 29 ga Disamba, 2025, an gurfanar da Malami, matarsa da dansa a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan tuhume-tuhume 16 da suka shafi safarar kudi da hada baki.

Source: Facebook
Saboda kasa cika sharuɗɗan beli a baya, Malami ya ci gaba da zama a tsare tun daga 8 ga Disamba, 2025 har sai da Kotun Babban Birnin Tarayya karkashin Mai shari’a Babangida Hassan ta tabbatar da halaccin tsarewar a ranar 18 ga Disamba.
Daga bisani, a ranar 7 ga Janairu, 2025 Mai shari’a Emeka Nwite ya bayar da beli ga Malami, matarsa da dansa kan Naira miliyan 500 kowannensu, tare da tsauraran sharuɗɗa.
Bayan kwanaki 12 da samun belin, Malami ya kammala sharuɗɗan sannan ya bar gidan yari, inda DSS ta sake cafke shi. Majiyoyi sun ce ba a sa ran za a sake shi nan kusa ba, domin binciken ka iya daukar watanni.
DSS ta sake damke Abubakar Malami
A wani labari, kun ji cewa tsohon Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari’a na Tarayya, Abubakar Malami, SAN, ya faɗa hannun Hukumar Tsaron Farar Hula (DSS) bayan ya fito daga kurkukun Kuje da ke Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an hukumar DSS sun cafke Abubakar Malami ne jim kaɗan bayan ya kammala sharuɗɗan belin da wata kotu ta ba shi a shari’ar da ke gudana a kansa.
Tun da farko dai, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ce ta cafke Malami tare da matarsa da ɗansa, bisa zargin safarar kuɗi da almundahana da suka kai biliyoyin Naira.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

