Hotunan Sanusi II bayan Ya Koma Jami’a, Ya Shiga Aji Sauraron Lakca da Dalibai

Hotunan Sanusi II bayan Ya Koma Jami’a, Ya Shiga Aji Sauraron Lakca da Dalibai

  • Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi II, ya koma karatun digiri a Jami’ar Northwest da ke jihar Kano, inda ya fara karbar lakca
  • Jami’ar ta ba Sarkin gurbin karatu na musamman ne a bangaren shari'a bisa la’akari da gogewarsa a shugabanci da hidimar jama’a
  • Zuwan Sarkin aji ya jawo farin ciki da mamaki a tsakanin dalibai, inda aka bayyana hakan a matsayin darasi kan muhimmancin neman ilimi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi II, ya koma karatun jami’a a ranar Talata 20 ga watan Janairun 2026.

Sarkin ya koma karatun ne a Jami’ar Northwest da ke Kano, a matsayin dalibi a matakin shekara ta biyu (Level 200) a fannin Shari’a.

Sanusi II ya koma makaranta domin yin digiri
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II yana karbar lakca a jami'ar Northwest. Hoto: Saifullah Ahs.
Source: Facebook

Sanusi II ya koma karatu a jami'a

Sarkin, wanda ya sanya doguwar riga baka da farin rawani, ya shiga aji tare da sauran dalibai domin halartar darasi ba tare da wani bambanci ba, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Dattawan Katsina sun shiga maganar sakin 'yan bindiga 70, sun zafafa kalamai

Rahotanni sun nuna cewa Sarkin ya zauna a bayan ajin kan kujerar mutane uku, yana sauraron darasi cikin nutsuwa kamar kowane dalibi.

Komawar tasa jami’a ta biyo bayan damar da jami’ar ta ba shi ta musamman a makon da ya gabata, inda aka ba shi gurbin karatu a bangaren shari'a.

Jami’ar ta bayyana cewa an ba Sarkin wannan dama ne bisa la’akari da dimbin gogewa da yake da ita a fannin shugabanci, tattalin arziki da hidimar jama’a.

An kafa Jami’ar Northwest a shekarar 2012, kuma tana daga cikin jami’o’i biyu da gwamnatin Jihar Kano ke mallaka.

Sarki Sanusi ya shiga lakca da dalibai a jami'a
Sarki Sanusi II a aji yana sauraron lakca. Hoto: Saifullahi Ahs.
Source: Facebook

Bangaren da Sanusi ya fi kwarewa a rayuwa

Duk da kasancewarsa mai digirin digirgir (PhD), Sarkin Kano wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ne, ya shahara wajen bayyana ra’ayoyi kan harkokin kasa.

An san Sarkin da kwarewa a fannin tattalin arziki da harkokin kudi, tare da jajircewarsa wajen tallafa wa ilimi da gyaran zamantakewa, kamar yadda The Nation ta ce.

Kasancewarsa a harabar jami’a ya jawo farin ciki a tsakanin matasan dalibai, inda wasu suka bayyana lamarin a matsayin babban darasi na neman ilimi ba tare da la’akari da matsayi ko shekaru ba.

Kara karanta wannan

Abba, Barau da hukumomi 2 da suka yi alkawarin nema wa Fatima da yaranta 6 adalci

Hotun Sarki Sanusu yayin lakca a jami'a

Hotunan Sarkin yayin halartar darasi sun kara yaduwa a shafukan sada zumunta, lamarin da ya jawo martani mai kyau daga jama’a da dama a fadin kasar.

Sarki Sanusi ya shiga lakca da dalibai a jami'a

Source: Facebook
Sarki Sanusi ya shiga lakca da dalibai a jami'a

Source: Facebook
Sarki Sanusi ya shiga lakca da dalibai a jami'a

Source: Facebook

Sanusi II ya jajanta mutuwar yan majalisar Kano

Kun ji cewa Masarautar Kano ta miƙa sakon ta’aziyya ga Gwamnatin Jihar Kano da Majalisar Dokoki bisa rasuwar ’yan majalisa biyu a rana daya.

Rasuwar Hon. Sarki Aliyu Daneji da Hon. Aminu Sa’adu Ungoggo ba zato ba tsammani ta jefa majalisar dokokin Kano cikin alhini da jimami.

Masarautar ta yabawa gudunmawar marigayan tare da roƙon Allah Ya gafarta musu Ya kuma bai wa al’umma haƙurin jure rashin mutanen kirki da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.