APC Ta Fayyace Wanda Zai Zama Jagora a Kano tsakanin Gwamna Abba da Ganduje

APC Ta Fayyace Wanda Zai Zama Jagora a Kano tsakanin Gwamna Abba da Ganduje

  • Jam'iyyar APC ta ce babu wata matsala da za a samu kan wanda zai zama jagoranta a Kano tsakanin Gwamna da Abdullahi Ganduje
  • Shugaban APC na reshen Kano, Abdullahi Abbas ya tabbatar da cewa Abba ne zai zama jagoran jam'iyya idan har ya shiga APC
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake rade-radin Abba Kabir Yusuf zai yanki katin zama cikakken 'dan APC a yau Talata ko gobe Laraba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abadullahi Abbas ya yi bayani kan wanda zai zama jagora idan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka.

Abdullahi Abbas ya tabbatar da cewa su na tsammanin gwamnan Kano zai yanki katin zama cikakken dan APC idan aka fara rijistar mambobi yau Talata ko gobe Laraba, 21 ga watan Janairu, 2025.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: NNPP ta hango makomarta a Kano bayan ficewar Gwamna Abba

Gwamna Abba Kabir.
Gwamna Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatin jihar Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A wata hira da ya yi da Freedom Radio, Abdullahi Abbas ya fayyace dambarwar da ake tunanin za ta iya tasowa idan Gwamna Abba ya sauya sheka zuwa APC.

Matsalar da za ta iya tasowa a jam'iyyar APC

A halin yanzu dai tsohon shugaban APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar, Dr Abdullaahi Umar Ganduje, shi ne jagoran jam'iyya a Kano.

Amma jita-jitar da shirin Abba na komawa APC musamman bayan ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta sa an fara tunanin wanda zai jagoranci jam'iyyar bayan komawar gwamna.

Rahotanni sun nuna cewa a al'ada da tsarin tafiyar da harkokin APC, gwamna shi ne jagoran jam'iya a jiharsa.

APC za ta ba Abba matsayin jagora a Kano?

Da yake bayani kan yadda abin zai kasance a Kano, Abdullahi Abbas ya ce maganar waye zai zama jagoran APC bayan mai girma gwamna ya sauya sheka ba abin damuwa ba ne.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Tinubu, an kara zuga Gwamna Abba kan rabuwa da Kwankwaso

Abbas ya ce a ka'ida da tsarin APC, kowane gwamna shi ne jagora a jiharsa, yana mai tabbatar da cewa hakan ba za ta canza ba a Kano idan Gwamma Abba ya koma APC.

Ya ce Gwamma Abba zai rike matsayinsa na jagoran APC a Kano, yayin da Ganduje zai zama uban jam'iyya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Tsohon shugaban APC na kasa.
Tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a hedkwatar jam'iyya da ke Abuja Hoto: @OfficialAPCNG
Source: Facebook

Wane matsayi Ganduje zai rike a APC?

Abdullahi Abbas ya ce:

"A ka'idar jam'iyyarmu, gwamna shi ne shugaba watau jagora amma mu a nan Kano, muna da jagora wanda shi ne tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
"Duk da na san su ba haka tsarinsu yake ba a can, amma mu idan Gwamna Abba ya shigo, shi ne jagoran APC a Kano, Ganduje kuma uban jam'iyya."

Kwankwaso ya fara tattaunawa da ADC

A wani labarin, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso na tattaunawa da 'yan adawa don duba yiwuwar kulla hadaka.

Rahotanni sun nuna cewa, Kwankwaso na gudanar da tattaunawa da manyan jagororin adawa a fadin ƙasar nan, a wani bangare na shirye-shiryen zaɓen 2027.

Wata majiya ta ce Kwankwaso ya fara tattaunawada jam'iyyar ADC, PDP da wasu manyan kusoshin adawa domin duba yiwuwar kulla hadaka da nufin kayar da APC a zabe mai zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262