Alfarmar da Gwamna Abba Kabir Ya Nema yayin Ganawa da Tinubu a Abuja
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gana da Shugaba Bola Tinubu a Abuja domin neman goyon bayansa a wasu bangarori
- Taron ya gudana ne a yayin da jita-jitar sauya shekarsa zuwa APC ke kara yaduwa da ke kara rikita siyasar jiharAbba
- Shugaba Tinubu ya tabbatar wa Gwamna Yusuf cewa gwamnatin tarayya a shirye take ta hada kai da Kano wajen magance matsalar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gudanar da wata muhimmiyar ganawa da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.
An yi ganawar a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, inda Abba ya gabatar da muhimman muradun gwamnatinsa.

Source: Twitter
A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Dawakin Tofa, ya fitar ya tabbatar da ganawar a shafinsa a Facebook da abubuwan da suka tattauna.
Abin da Abba ya tattauna da Tinubu
Sanusi Dawakin Tofa ya bayyana cewa tattaunawar ta mayar da hankali ne kan tsaro, ababen more rayuwa da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin Kano da gwamnatin tarayya.
Ganawar ta gudana ne a daidai lokacin da ake ta yada rade-radin yiwuwar gwamnan sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, lamarin da ke jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasar jihar.
Sanarwar ta ce, duk da cewa taron ya kasance na sirri, Gwamna Yusuf ya yi amfani da damar wajen sanar da Shugaban Kasa kalubale da dama da jihar Kano ke fuskanta, musamman tabarbarewar tsaro a wasu kananan hukumomi.

Source: Facebook
Sakon godiya, roko ga Bola Tinubu
Haka kuma, Gwamna Abba Yusuf ya gabatar da manufar ci gaban Kano, inda ya jaddada bukatar aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa da za su bunkasa tattalin arziki.
Ya gode wa Shugaban Kasa bisa sa hannun gwamnatin tarayya a aikin titin Wujuwuju, wanda ya bayyana a matsayin muhimmin aiki da zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da bunkasar tattalin arziki.
Gwamnan ya sanar da Tinubu game da kisan wata mata da ’ya’yanta da aka yi kwanan nan, inda ya bukaci daukin gaggawa daga gwamnatin tarayya domin kare rayukan fararen hula.
Abba Kabir ya bayyana rawar da Rundunar Tsaron Unguwanni ta Kano ke takawa wajen tallafa wa hukumomin tsaro, tare da bukatar karin hadin gwiwa da jami’an tsaron tarayya.
Gwamnan ya kuma bukaci goyon bayan Shugaban Kasa domin gaggauta aiwatar da ayyukan tarayya a Kano, tare da tabbatar da cewa jihar na cin gajiyar shirye-shiryen gwamnatin tarayya.
A nasa jawabin, Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa Gwamna Yusuf cewa gwamnatin tarayya za ta yi aiki kafada da kafada da Kano domin magance matsalar tsaro da kuma samar da ci gaba mai dorewa.
NNPP ta magantu kan sauya shekar Abba
A wani labarin, alamu na ci gaba da nuna cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zargin sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC.
Kakakin jam'iyyar NNPP ta kasa, Ladipo Johnson, ya fadi makomar jam'iyyar a zaben shekarar 2027 idan Gwamna Abba ya koma APC.
Ladipo Johnson ya bayyana cewa ko a zabubbukan shekarar 2019 da 2023, jam'iyyar NNPP ta samu nasara a Kano duk da cewa ba ta da gwamna mai ci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

