Mutanen Dorayi Sun Fadi Ainihin Abin da Ya Faru kan Kisan Fatima da Yaranta 6 a Kano

Mutanen Dorayi Sun Fadi Ainihin Abin da Ya Faru kan Kisan Fatima da Yaranta 6 a Kano

  • Makwbtan gidan da aka kashe uwa da yaranta shida a jihar Kano sun musanta zargin da ake yi musu na sakaci da rashin kai dauki da wuri
  • Mazauna unguwar Dorayi Chiranci sun bayyana cewa cikin 'yan dakiku da ankara da abin da ke faruwa suka zagaye gidan Fatima
  • A cewarsu, su suka kira jami'an tsaro, kuma suka damka masu Umar da wani mai suna Wawa, wanda yana cikin wadanda ake zargi da kisan gillar
  • suka aikata kisan gillar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Mazauna unguwar Dorayi Chiranci da ke cikin birnin Kano sun yi martani ga masu cewa akwai laifin makwafta a kisan gillar da aka yi wa matar aure da yaranta shida.

Mutanen unguwar sun bayyana cewa bayan faruwar lamarin, mutane sun kawo dauki, suka zagaye gidan cikin kankanin lokaci tare da kama wadanda suka aikata danyen aikin.

Kara karanta wannan

'Sun yi amfani da keken dinki,' An ji yadda aka kashe Fatima da yaranta 6 a Kano

Jihar Kano.
Taswirar jihar Kano a Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda Dokin Karfe TV ta wallafa a Facebook, an ji wani dan unguwar na ba labarin abin da ya faru.

Mutumin ya bayyana cewa suna cikin unguwa lokacin da lamarin ya faru, amma ba su ankara ba sai da yaran matar suka fara ihu, ita kuma Fatima tana rokon a kyale su.

Makwafta sun kai dauki gidan Fatima

Ya ce wasu masu fenti a unguwa da suka kunna na'urar jin wakoki ne suka fara ankara, suka kashe abin da suke ji don tabbatar da kururuwar yaran da suka ji.

Mutumin ya ce:

"A nan bayan layi, yara suka fara ji suka ce aljanu na fada, to akwai wata mace da ta zo wucewa, ita ba ta dauki maganar yaran da gaske ba, amma da wasu masu fenti suka ji, sai suka kashe wakokin da suka kunna.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya bada umarni game da kisan matar aure da yaranta 6 a Kano

"Suka ji ana wayyo Allah, Umar kar ku kashe ni, Umar zan maka bayani, nan take masu fentin suka zagayo suka gayawa Mario, shi kuma yana lekowa ya hango Umar da shi da Wawa a sama, ya fara ihu barawo.
"Yana yin ihu daya, biyu, cikin dakiku da ba su wuce 15 ba duk unguwar nan kowa ya fito, muka zagaye gidan, duk mun gansu, masu cewa an bari sun gudu karya ne, mu muka kama su."
Fatima da iyalanta.
Fatima da 'ya'yanta tare da mahaifinsu Hoto: Muhammad Ahmad
Source: Facebook

Yadda mutane suka taimaki jami'an tsaro

Makwabcin kuma musanta ikirarin cewa makasan sun yi shigar mata, yana mai cewa su suka kira jami'an tsaro suka zo, suuka tafi da wadanda ake zargin kar mutane su dauki doka a hannunsu, in ji rahoton The Nation.

Ya kuma maida martani ga yan soshiyal midiya da ke zagin makwabtan Fatima, inda ya ce cikin dakiku suka zagaye wurin amma tsagerun sun riga sun aikata mugun nufinsu.

Kafin yanzu, rahoto ya gabata cewa mutanen unguwar sun yi gum a lokacin da abin yake faruwa, kuma a karshe aka cafko wadanda ake zargi da laiifin kisan a wata unguwa.

Gwamnatin Kano za ta gurfanar da su Umar

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa za ta jagoranci shigar da ƙara kan kisan matar aure da ƴaƴanta shida a Dorayi Chiranchi.

Kara karanta wannan

'Wanda aka kashe matarsa da 'ya'yansa 6 a Kano na bukatar taimako'

Lamarin ya girgiza zukatan jama’a tare da jefa daukacin jihar cikin alhini mai tsanani a yayin da har yanzu, mutane ke cikin jimamin faruwar lamarin.

Gwmnati ta bayyana kisan a matsayin aikin rashin tausayi da rashin imani da ya girgiza tunanin al’ummar Kano, tare da haifar da fargaba da damuwa game da tsaron rayuka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262