DSS Ta Sake Damke Abubakar Malami bayan Ya Samu Beli daga Kurkukun Kuje
- Tsohon Ministan Shari’a na Tarayya, Abubakar Malami, SAN, ya sake shiga hannun jami’an tsaro bayan hukumar DSS ta kama shi a Abuja
- Kamen ya zo ne jim kaɗan bayan Malami ya cika sharuɗɗan beli da aka ba shi a gidan yarin Kuje, yayin da bincike kan zarge-zargen ta'addanci
- Hukumomin tsaro sun jaddada cewa zarge-zargen ta’addanci manyan laifuffuka ne da ba za a yi wasa da su ba, komai girman wanda ake tuhuma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari’a na Tarayya, Abubakar Malami, SAN, ya shiga hannun Hukumar Tsaro ta Farar Hula (DSS).
An kama Malami ne bayan ya fito daga gidan yarin Kuje da ke Abuja, bayan ya cika sharuɗɗan belin da aka ba shi a wani shari’a da ke gudana a kansa.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa tun da farko, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ce ta kama Malami tare da matarsa da ɗansa, bisa zargin safarar kuɗi da almundahana.
Hukumar EFCC na tuhumar Abubakar Malami
Daily Post ta wallafa cewa duk da kama su, kotu ta ba kowane ɗaya daga cikinsu beli na Naira miliyan 500, lamarin da ya ba su damar fita daga tsarewa yayin da ake ci gaba da bincike.
Majiyoyi sun bayyana cewa bayan fitar Malami daga gidan yari, DSS ta kama shi domin gudanar da wani sabon bincike.
Wannan sabon bincike ya samo asali ne daga gano makamai a gidansa da ke jihar Kebbi, abin da jami’an EFCC suka ce sun gano yayin wani bincike da suka gudanar a gidan.
Duk da ƙoƙarin da aka yi na samun martani daga DSS, hukumar ta ƙi yin wata sanarwa a hukumance dangane da kamun.
An tabbatar da kama Abubakar Malami
Sai dai wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewa DSS ta yi ram da Malami SAN a yayin da ya fito daga gidan yarin Kuje.
Majiyar ta ce:
“Eh, gaskiya ne DSS ta kama Abubakar Malami, SAN. Akwai koke-koke da dama a kansa da suka shafi zargin tallafa wa ta’addanci. Ta’addanci da tallafa masa babban laifi ne a duk faɗin duniya.”
Majiyar ta tunatar da cewa a lokacin da Malami yake rike da muƙamin Babban Lauyan Ƙasa da Ministan Shari’a, ya sha jaddada cewa gwamnatin ba za ta raga wa duk wanda aka kama da alaka da ta'addanci ba.

Source: Twitter
Wata majiya ta ci gaba da cewa babu wata gwamnati mai kishin ƙasa da za ta yi shiru ko ta juya baya ga manyan zarge-zargen tallafa wa ta’addanci da aka yi wa kowane mutum, ko da kuwa yana da matsayi mai girma.
A cewar majiyar, a Najeriya DSS ce ke da alhakin binciken zarge-zargen ta’addanci da tallafa masa, don haka ya dace a bar hukumar ta gudanar da aikinta yadda doka ta tanada.

Kara karanta wannan
Abba, Barau da hukumomi 2 da suka yi alkawarin nema wa Fatima da yaranta 6 adalci
Kotu ta bada belin Abubakar Malami
A wani labarin, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bayar da beli ga tsohon Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, tare da matarsa da ɗansa.
Kotun ta kakaba tsauraran sharuda, ciki har da beli na Naira miliyan 500 ga kowane daga cikin waɗanda ake tuhuma, da kuma sharuɗɗan kadarori a manyan unguwannin birnin tarayya kafin a bada belin.
Mai shari’a Emeka Nwite ya kuma hana Malami da sauran waɗanda ake tuhuma yin balaguro zuwa ƙasashen waje sai da izinin kotu, domin tabbatar da bin sawun shari’a yadda ya kamata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

