Yadda Tubabbun 'Yan Bindiga Suka Taimaka Aka Kashe Tsageru 50 a Katsina
- Dakarun sojojin saman Najeriya sun samu nasarar hallaka tsagerun 'yan bindiga bayan sun kai musu farmaki a jihar Katsina
- Sojojin sun ragargaji 'yan bindigan ne lokacin da suka dawo daga kai hari a cikin wani yanki na jihar Kano
- Nasarar da sojojin suka samu ta zo ne bayan wata gagarumar hubbasa da wasu tubabbun 'yan bindiga suka yi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Dakarun sojojin saman Najeriya sun hallaka akalla ‘yan bindiga 50 da ke kai hare-hare a yankunan Musawa, Matazu da Danmusa na Katsina, da kuma yankin Tsanyawa a jihar Kano.
Sojojin saman sun samu nasarar ne sakamakon samamen da suka kai kai tsagerun 'yan bindigan.

Source: Facebook
Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar Katsina, Nasiru Mu’azu Danmusa, ne ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho da jaridar Daily Trust a safiyar Litinin, 19 ga watan Janairun 2026.
Tubabbun 'yan bindiga sun yi taimako
A cewarsa, an kai harin ne bisa sahihin bayanan sirri da aka samu, tare da taimakon wasu tsofaffin ‘yan bindiga da suka tuba, wadanda suka bayar da muhimman bayanai ga jami’an tsaro.
Nasir Muazu Danmusa ya bayyana cewa ‘yan bindigan da aka kashe mayaka ne da ke biyayya ga Baidu, wani shahararren jagoran ‘yan bindiga da ke adawa da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a Danmusa da wasu sassan jihar Katsina.
Ya ce an kashe su ne a yankin karamar hukumar Matazu yayin da suke dawowa daga munanan hare-hare da suka kai wa al’umma a wasu yankunan karamar hukumar Tsanyawa ta jihar Kano.
Gwamnati za ta kara zage damtse
Duk da yarjejeniyar zaman lafiya da ke aiki a wasu yankuna, kwamishinan ya jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da ‘yan bindiga.
“Ta hanyar musayar bayanan sirri da hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro na jihohin Kano da Katsina, tare da goyon bayan al’umma da kuma tsofaffin ‘yan bindiga da suka tuba, muna samun nasarori masu yawa."

Kara karanta wannan
Sojojin saman Najeriya sun yi ruwan bama bamai a Borno, mutane fiye da 40 sun mutu
- Nasiru Muazu Danmusa
Ya tabbatar wa da al’umma cewa za a ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’adda har sai an kawar da dukkan barazanar tsaro a jihar.
Sojojin sama sun kona 'yan bindiga kurmus
Wasu shaidu da suka nemi a sakaya sunayensu saboda dalilan tsaro sun tabbatar da cewa an kashe ‘yan bindiga da dama ta hanyar hare-haren sama yayin da suke shirin kai farmaki kan gonaki a tsakanin kauyukan da ke tsakanin Matazu da Danmusa.

Source: Original
Wani daga cikin shaidun ya ce gawarwakin ‘yan bindigar sun kone kurmus, amma an gane su ta hanyar muggan makamai da aka samu a wurin, ciki har da alburusai, harsasai, wukake, adda da kuma wayoyin hannu da aka sace.
Mazauna yankin sun bayyana kwarin gwiwa cewa wannan yaki da ‘yan bindiga zai yi nasara, amma sun bukaci gwamnati da ta mayar da hankali wajen sake gina al’ummomin da aka lalata sakamakon shekaru na ta’addanci.
Sun ce sake gina kauyuka, tare da shirin sake haɗa tsofaffin ‘yan bindiga cikin al’umma, gyara rayuwar wadanda abin ya shafa da kuma tallafa musu, na da matukar muhimmanci wajen samar da dorewar zaman lafiya a yankin.
Dattawan Katsina sun magantu kan sakin 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Katsina Community Security Initiative ta yi magana kan shirin sakin wasu 'ya bindiga da aka cafke.
Jagoran kungiyar, Dr Bashir Kurfi, ya bayyana rashin amincewarsa da duk wani yunkuri na sakin tsagerun, yana mai cewa hakan barazana ce ga tsaron al’umma.
Ya ce a bayyane yake cewa sakin ’yan ta’adda, musamman wadanda aka kama da laifuffukan fyade da kisan kai, ba zai kawo zaman lafiya ba.
Asali: Legit.ng

