Shin da Gaske Mahaifiyar Nuhu Ribadu Ta Rasu? An Ji Gaskiyar Zance

Shin da Gaske Mahaifiyar Nuhu Ribadu Ta Rasu? An Ji Gaskiyar Zance

  • Wasu rahotanni masu ikirarin cewa mahaifiyar mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ta rasu a ranar Litinin, 19 ga watan Disamban 2026
  • Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewa ya samu kiraye-kiraye daga abokai da makusanta domin jajanta masa kan lamarin
  • Sai dai, ya bayyana cewa ba a kawo rahoton yadda ya kamata, domin ba a fadi gaskiyar abin da ya faru a cikinsa ba

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa mahaifiyarsa ta rasu a ranar Litinin, 19 ga watan Janairun 2026.

Duk da yadda lamarin ya yi ta yawo a yammacin ranar Litinin, Nuhu Ribadu ya bayyana cewa gaba daya yadda aka fitar da labarin ba haka gaskiyar abubuwa suke ba.

Kara karanta wannan

Aikin gama ya gama, Shugaba Tinubu ya shiga ganawa da gwamnan Kano a Abuja

Nuhu Ribadu ya ce mahaifiyarsa ta dade da rasuwa
Malam Nuhu Ribadu tare da matar da aka ce mahaifiyarsa ce ta rasu Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Facebook

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Litinin, 19 ga watan Janairun 2026.

Batun rasuwar mahaifiyar Nuhu Ribadu

A rahoton da aka fitar, an bayyana cewa An ce Hajiya Aisha Mamma ta rasu da safiyar Litinin 19 ga watan Janairun 2025 tana da shekaru 86 a duniya bayan fama da jinya.

Hakazalika, an bayyana cewa Marigayiyar, wadda aka fi sani da Hajja Mamma, ita ce kuma mahaifiyar Sarkin Fufore a Jihar Adamawa, Mai Martaba Sani Ribadu.

Me Ribadu ya ce kan rasuwar mahaifiyarsa?

A sakon da ya fitar, Nuhu Ribadu ya bayyana cewa ya samu kiraye-kiraye da dama kan batun cewa mahafiyarsa ta rasu.

Sai dai, ya bayyana cewa babu kamshin gaskiya a cikin rahotannin da ke cewa Allah ya karbi ran mahaifiyarsa a ranar Litinin, 19 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Tazarce: Gwamna ya jero dalilan da za su sanya ƴan Kaduna su zabi Tinubu a 2027

“Na samu kiraye-kiraye da saƙonni da dama daga abokai da makusanta bayan wani rubutu da ya bazu a kafafen intanet, wanda ba daidai ba ne, yana ikirarin cewa mahaifiyata ta rasu a ranar Litinin, 19 ga Janairu, 2026."
"Duk da cewa ina matuƙar godiya ga kowa da ya kira ko ya aiko da sakon ta’aziyya, ya zama wajibi in fayyace gaskiyar lamarin."
"Wannan labari karya ne kuma ya ruɗa jama’a. Mahaifiyata, Allah ya jikanta, ta rasu shekaru 28 da suka gabata, don haka ba za a ce ta rasu a ranar Litinin ba."
"Wadda ta rasu a ranar Litinin ita ce Hajja Mamma Sulaiman Ribadu, matar marigayi kawuna. Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya ji ƙan ranta, kuma Ya sanya ta cikin Aljannatul Firdausi."
"Muna matuƙar godiya ga dukkan waɗanda suka nuna alhini ga iyalinmu a wannan lokaci na jimami. Allah Ya saka muku da alheri mai yawa.”

- Nuhu Ribadu

Nuhu Ribadu ya yi magana kan rasuwar mahaifiyaraa
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Malam Nuhu Ribadu Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Facebook

An bukaci Tinubu ya sauya Ribadu

A wani labarin kuma, kun ji cewa an bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya sauya Nuhu Ribadu daga kan mukaminsa.

Sanatan Osun ta Gabas, Francis Fadahunsi, ya yi wannan kiran yayin da yake bukatar Shugaba Tinubu ya ci gaba da gyara tsarin tsaro.

Sanatan ya bukaci gyaran ne ta hanyar nada wani tsohon soja a matsayin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA).

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng