Abubuwan da Abba Kabir Ya Tattauna da Tinubu ana Maganar Shigarsa APC
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi ganawar sirri da Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin tattauna muhimman batutuwan tsaro da ci gaban jihar
- Rahotanni sun ce sun tattauna matsalolin tsaro da ke addabar wasu kananan hukumomi tare da neman karin hadin gwiwa daga gwamnatin tarayya
- Haka kuma, shugabannin sun mayar da hankali kan manyan ayyukan more rayuwa da ake sa ran za su bude kofar bunkasar tattalin arziki a jihar Kano
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja, FCT – Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gudanar da wata ganawa ta musamman da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ganawar ta mayar da hankali ne kan kalubalen tsaro, manyan ayyukan more rayuwa da kuma yadda Kano za ta kara amfana daga shirye-shiryen gwamnatin tarayya.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da tattaunawar ne a cikin wani sako da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature D-Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin gwamnan zai koma jam'iyyar APC daga NNPP mai mulki a jihar Kano.
Tattaunawar Abba da Tinubu kan tsaro
A yayin ganawar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar wa Shugaba Tinubu da cikakken bayani kan halin tsaro a wasu sassan Jihar Kano.
Gwamnan ya bayyana cewa matsalolin tsaro sun kara tsananta a wasu kananan hukumomi, lamarin da ke bukatar dauki na gaggawa.
Abba Kabir ya jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne ginshikin kowace gwamnati, inda ya nemi karin goyon bayan gwamnatin tarayya domin karfafa ayyukan tsaro a jihar.
Ya kuma ambaci kisan gillar da aka yi wa wata matar aure da ’ya’yanta a baya-bayan nan, yana mai bayyana hakan a matsayin abin bakin ciki da ke bukatar daukar matakan da suka dace.

Source: Facebook
Wasu abubuwan da Abba ya fadawa Tinubu
Gwamnan ya bayyana rawar da rundunar Kano State Neighbourhood Watch Corps ke takawa wajen tallafa wa jami’an tsaro na hukuma.
Sai dai ya jaddada cewa akwai bukatar kara dankon zumunci da hadin gwiwa tsakanin rundunar da hukumomin tsaro na tarayya domin samun sakamako mai dorewa.
Baya ga batun tsaro, gwamnan ya tattauna ajandar ci gaban Kano, inda ya mayar da hankali kan manyan ayyukan more rayuwa.
Ya nuna godiya kan taimakon gwamnatin tarayya a aikin titin Wujuwuju, yana mai bayyana shi a matsayin muhimmin mataki wajen bunkasa harkokin kasuwanci da samar da ayyukan yi.
Martanin Tinubu ga Abba Kabir Yusuf
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa gwamnan cewa gwamnatin tarayya a shirye take ta yi aiki kafada da kafada da Jihar Kano.
Shugaban ya nuna cewa hadin gwiwa tsakanin matakan gwamnati daban-daban shi ne mabuɗin cimma tsaro da ci gaba, tare da jaddada aniyar tallafawa Kano domin cimma wadannan manufofi.

Kara karanta wannan
Abba, Barau da hukumomi 2 da suka yi alkawarin nema wa Fatima da yaranta 6 adalci
An gargadi Abba kan shirin shiga APC
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan jam'iyyar APC a jihar Kano sun yi martani kan rade-radin sauya shekar Abba Kabir Yusuf.
Wasu daga cikin 'yan jam'iyyar sun bayyana cewa ko da gwamnan ya shiga cikinsu, zai bi tsarin da suka riga suka gindaya ne.
Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda ya bukaci gwamnan da ya koma wajen mai gidansa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso maimakon shiga APC.
Asali: Legit.ng

