Kalaman da Aka Ji Tinubu Ya Fada bayan Tabbatar da Rasuwar Sheikh Muhammad Bashir Saliu

Kalaman da Aka Ji Tinubu Ya Fada bayan Tabbatar da Rasuwar Sheikh Muhammad Bashir Saliu

  • A yau Litinin, 19 ga watan Janairu, 2026 aka tabbatar da rasuwar babban limamin Ilorin, Sheikh Muhammad Bashir Saliu
  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mika sakon ta'aizyya ga iyalai, masarautar Ilorin da daukacin al'ummar jihar Kwara bisa wannan rashi
  • Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin malamin Musulunci da ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada ilimi da tarbiyyar matasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna matukar alhininsa kan rasuwar Sheikh Muhammad Bashir Saliu, Babban Limamin Ilorin, wanda ya rasu yana da shekaru 75.

Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin babban malamin Musulunci wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga ayyukan hidima, da kuma inganta hadin kai a cikin al'umma.

Sheikh Muhammad Bashir.
Babban limamin Ilorin a jihar Kwara, Sheikh Muhammad Bashir Saliu Hoto: Ilorin Emeirate
Source: Twitter

Hakan dai na kunshe ne cikin wani sako na ta’aziyya da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Litinin, in ji The Nation.

Kara karanta wannan

Babban limamin Ilorin, Sheikh Saliu ya rasu bayan shekaru 43 ya na jan Sallah

Bola Tinubu ya yi jimamin rasuwar Limamin Ilorin

Tinubu ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, Mai Martaba Sarkin Ilorin, Ibrahim Sulu-Gambari, da Majalisar Masarautar Ilorin, da daukacin al'ummar musulmi na Jihar Kwara kan wannan babban rashi.

Bola Tinubu ya ce:

“Sheikh Muhammad Bashir Saliu bawan Allah ne, mai kokarin dinke baraka da hada kai tsakanin al'umma, wanda hikimarsa, kankan da kansa, da jajircewarsa wajen hadin kai suka sa mutane na kowane bangare ke kaunarsa.”

Gudunmuwar da limamin ya bada a Kwara

A cewar Tinubu, marigayi Babban Limamin ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin addinai da ci gaban al'umma, yayin da ya sadaukar da rayuwarsa wajen ilimantarwa da tarbiyyar matasa.

“Al'ummar Musulmi ba za su taba mancewa da gudunmawar da Sheikh ya bayar ba wajen samar da daidaito tsakanin addinai, ci gaban al'umma, da tarbiyyar matasa ta hanyar ilimi ba,” in ji Tinubu.
Sheikh Muhamma Bashir.
Babban limamin Ilorin, Sheikh Muhammad Bashir Saliu da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Shugaba Tinubu ya nema masa rahama

Kara karanta wannan

Azumi saura wata 1: Sarkin Musulmi ya ba da umarnin duba watan Sha'aban 1447

Daga karshe, Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya jikan malamin, Ya kuma sanya shi a Aljannar Firdausi, sannan Ya bai wa iyalansa, dalibansa, da daukacin al'ummar Musulmi hakurin jure wannan rashi.

Sheikh Muhammad Bashir Saliu ya kasance babban limami na 12 a tarihin Masarautar Ilorin, kuma ya shafe shekaru sama da 40 yana wannan aiki tun bayan nada shi a shekarar 1983.

An gudanar da sallar jana'izarsa a yau Litinin, 19 ga Janairu, 2026, a fadar Sarkin Ilorinda ke jihar Kwara, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Tinubu ya yi ta'ziyyar rasuwar Imam Abubakar

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhini da jimami kan rasuwar Malam Abdullahi Abubakar daga jihar Filato.

Imam Abubakar ya shahara a ciki wajen Najeriya bayan da ya ɓoye tare da kare Kiristoci sama da 200 a shekarar 2018, a lokacin rikicin addini da ya girgiza Jihar Filato.

Tinubu ya ce rayuwar marigayin ta kasance shaida ta gaskiya, jarumtaka da girmama rayuwar kowane ɗan Adam ba tare da duba addininsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262