Abin da Gwamnati da 'Yan Sanda Suka Ce kan Batun Sace Mutane Sama da 100 a Cocin Kaduna

Abin da Gwamnati da 'Yan Sanda Suka Ce kan Batun Sace Mutane Sama da 100 a Cocin Kaduna

  • Wasu rahotanni sun yadu masu cewa 'yan bindiga sun yi awon gaba da masu ibada a wani coci da ke jihar Kaduna
  • Kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna, Alhaji Muhammad Rabiu, ya fito ya yi gamsashshen bayani kan lamarin
  • Shugaban karamar hukumar da aka ce lamarin ya auku, ya bayyana cewa ya je da 'yan sanda wurin da ake cewa an kai harin

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Kwamishinan ’yan sanda na Kaduna, Alhaji Muhammad Rabiu, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa 'yan bindiga sun sace masu ibada a wani coci a jihar.

Kwamishinan 'yan sandan ya bayyana rahotannin da ke cewa an sace masu ibada 163 a karamar hukumar Kajuru a matsayin karya tsagwaron ta.

'Yan sanda sun yi magana kan harin Kaduna
Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya da jami'an rundunar Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar tsaro ta Jiha da aka gudanar a Sir Kashim Ibrahim House ranar Litinin, 19 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Kisan Fatima: Sheikh Daurawa ya yi magana mai ratsa zuciya kan ta'addancin da aka yi a Kano

Kwamishinan 'yan sandan Kaduna ya yi bayani

Kwamishinan ’yan sandan ya kalubalanci duk wanda ke yin wannan ikirari da ya fito ya bayyana sunayen waɗanda ake zargin an sace tare da bayar da cikakkun bayanansu.

Ya kuma yi gargaɗi kan duk wani yunƙuri na tayar da zaune-tsaye da kawo cikas ga zaman lafiyar da jihar Kaduna ke morewa a halin yanzu, rahoton jaridar Vangurd ya tabbatar da hakan.

Abin da shugaban karamar hukuma ya ce

Shi ma da yake magana, shugaban karamar hukumar Kajuru, Dauda Madaki, ya ce bayan jin jita-jitar harin, ya tattara ’yan sanda da sauran jami’an tsaro zuwa yankin Kurmin Wali, amma suka gano cewa babu wani hari da ya faru.

“Mun ziyarci cocin da ake cewa an yi satar mutanen a cikinsa, amma ba mu ga wata alamar hari ba. Na tambayi hakimin kauyen, Mai Dan Zaria, ya ce babu wani abu makamancin hakan da ya faru."
“Haka kuma na kira shugaban matasan yankin, Bernard Bona, wanda ’yan jaridar da suka raka ni suka yi hira da shi, shi ma ya ce babu wani abu makamancin haka da ya faru."

Kara karanta wannan

Tazarce: Gwamna ya jero dalilan da za su sanya ƴan Kaduna su zabi Tinubu a 2027

“Saboda haka, ina kalubalantar duk wanda ke cewa an sace mutane da ya fito ya bayyana sunayensu. Ina jiran wannan jerin sunaye, amma har yanzu babu wanda ya kawo ko suna ɗaya."

- Dauda Madaki

Madaki ya kara da cewa yana da yakinin cewa jita-jitar satar mutanen na ɗauke da hannun wasu da ba sa jin daɗin zaman lafiyar da Kajuru ke samu tun bayan shigowar gwamnatin yanzu.

An ba mutane shawara

Hon. Dauda Madaki ya shawarci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum cikin lumana.

Ya kuma bukace su da su rika kai rahoton duk wani motsi da ya ba su shakku ko masu yaɗa jita-jita ga jami’an tsaro.

'Yan sanda sun ce ba a sace masu ibada a cocin Kaduna ba
Taswirar jihar Kaduna, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

CAN ta ce an sace masu ibada a coci

Tun da farko, Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Arewa, Fasto John Hayab, ya yi zargin cewa an sace masu ibada daga cocin Cherubim da Seraphim na 1 da kuma Cherubim da Seraphim na 2, duk a cikin Kajuru.

Hayab ya ce maharan sun kutsa cikin cocin ne yayin da ake gudanar da ibada, suka kulle ƙofofi tare da tafiya da masu ibadar zuwa cikin daji.

Kara karanta wannan

Yadda yaron shago ya hallaka mai gidansa makonni 3 bayan aurensa a Gombe

Gwamnatin Kaduna ta yi magana

Sai dai a martaninsa, Kwamishinan harkokin tsaro na cikin gida da harkokin cikin Gida, Sule Shuaibu (SAN), ya ce shugaban CAN da sauran shugabannin addini sun tuntubi mazauna yankin da ake cewa an yi satar mutanen.

“Sun gano cewa abin da aka gayawa jama’a gaba ɗaya karya ce. Gwamnatin jihar Kaduna ba ta da sassauci ko kaɗan wajen yaki da aikata laifuffuka.”

- Sule Shuaibu

'Yan bindiga sun kai hari a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a wani kauyen jihar Sokoto.

'Yan bindigan sun kai harin ne a kauyen Kyara, wani kauye mai nisa da ke kan iyaka a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigan sun hallaka akalla mutane bakwai, raunata wasu tare da yin awon gaba da mutane da dama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng