Kisan Fatima: Sheikh Daurawa Ya Yi Magana Mai Ratsa Zuciya kan Ta'addancin da Aka Yi a Kano

Kisan Fatima: Sheikh Daurawa Ya Yi Magana Mai Ratsa Zuciya kan Ta'addancin da Aka Yi a Kano

  • Shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim.Daurawa ya yi magana kan kisan gillar da aka yi wa wata matar aure
  • Sanannen malamin addinin Musuluncin ya bayyana cewa kisan matar da 'ya'yanta guda shida ya yi muni matuka
  • Sheikh Daurawa ya bayyana cewa lamarin ya kara nunawa a fili yadda matsalar rashin tsaro ke kara tabarbarewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Sanannen malamin addinin Musulunci kuma shugaban hukumar Hisbah a jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa, ya nuna takaicinsa kan yadda matsalar rashin tsaro ke kara taɓarɓarewa.

Sheikh Aminu Daurawa ya koka da cewa yanzu gidajen jama'a sun koma wuraren da babu tsaro.

Daurawa ya koka kan kisan da aka yi wa matar aure a Kano
Shugaban hukumar Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Daurawa Hoto: Imam Dr. Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

Daurawa ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da aka sanya a shafinsa na Facebook yayin da yake martani kan kisan wata mata mai suna Fatima da ’ya’yanta shida.

Kara karanta wannan

"Ba za mu lamunta ba:" Gwamna Abba ya yi alkawarin nema wa fatima da yaranta adalci

Wasu matasa ne dai suka yi wa matar da 'ya'yanta kisan gilla a yankin Dorayi Chiranchi na birnin Kano.

Me Daurawa ya ce kan kisan Fatima da 'ya'yanta?

Malamin ya ce lamarin ya girgiza shi matuƙa har ya kasa yin barci saboda tsananin bakin ciki da damuwa.

“Jiya mun kwana cikin bakin ciki da bacin rai da damuwa. Na so ace an fara wannan wa'azin karfe 10:00 kamar yadda aka fada, amma barcin ma bai zo ba."

- Sheikh Aminu Daurawa

A cewarsa, jami’an Hisbah sun aiko masa da bayanai da hotunan abin da ya faru, wanda ya ce sun yi muni saboda tsananin rashin imanin da aka nuna.

“Ka yi tunanin ka dawo gida daga wurin lakca, ofis, makaranta, gona ko aiki, ka je ka ga an shimfide maka matarka da ’ya’yanka gabadaya wani dan ta'adda ya yanka maka su, har ya zuba wasu a cikin rijiya."

- Sheikh Aminu Daurawa

Kisan Fatima ya girgiza Daurawa

Daurawa ya bayyana lamarin a matsayin wani abu da ba a taɓa ganin irinsa ba ta fuskar tsananin zalunci.

Kara karanta wannan

Pantami ya yi mamakin kisan gilla da tsakar rana a Kano, ya yi masu mummunar addu'a

“Na yi tunani ai Fir’auna, ya yi irin wannan, amma sai na ga na Fir'auna bai kai munin wannan ba, domin Fir'auna ba ya yanka mata, maza kawai yake yankawa."
"Fir'auna ma ya fi wadannan 'yan ta'addan tausayi, domin Fir'auna maza yake kashewa baya kashe mata."
"Sannan sai na yi tunani ai a zamanin jahiliyya ana kashe yara, sai nan ma na ga shi ma bai kai munin wannan ba, domin su kuma mata suke kashewa suke barin maza."
"Don haka wanda ya yi ta'addanci ya hada yara maza da mata da uwarsu ya kashe su, ni ban taba ganin irin wannan ta'addancin ba a tarihi, ban taba ganin rashin imani irin wannan ba."
"Ban taba ganin rashin tausayi irin wannan ba, ban taba ganin rashin ta ido irin wannan ba. Uwa a gaban 'ya'yanta ka kashe ta, ka kashe su, wannan babbar masifa ce."
"Muna cikin halin kakanikayi, kenan yanzu gidanmu babu tsaro, hanyoyinmu babu tsaro. Ba mu da tsaro a gida, ka tafi wani wuri, wani ya zo har gida ya kashe maka iyali."

- Sheikh Aminu Daurawa

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗan kasar waje a Najeriya bayan hallaka ɗan sanda

Dairawa ya koka kan kisan gilla a Kano
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da 'yaran Fatima da aka kashe a Kano Hoto: Imam Dr. Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

Daurawa ya koka kan rashin tsaro

Ya ce abin da ya faru ya nuna cewa rashin tsaro ya kai wani mataki mai matukar firgita jama'a.

Malamin ya ɗora alhakin ƙaruwa da laifukan tashin hankali kan rashin tarbiyya da sakacin al’umma, yana mai jaddada cewa masu aikata laifukan ba baki ba ne.

Daurawa ya ce yawaitar irin waɗannan laifuffuka, ciki har da lokutan da mutane ke kashe iyayensu, ma’aurata ko ’yan uwansu, ya kamata ya tayar da hankalin duk mai imani.

“Duk wanda ya ji wannan labari yana da imani, zuciyarsa za ta girgiza, musamman idan ya yi tunanin ace lamarin ya faru da shi."

- Sheikh Aminu Daurawa

Ya yi kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar da cafke duk waɗanda ke da hannu a kisan, tare da roƙon bangaren shari’a da ya gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da adalci.

Ya nuna yatsa ga gwamnoni

Malamin ya kuma soki gwamnonin jihohi kan jinkirin sanya hannu kan aiwatar da hukuncin kisa ga waɗanda kotu ta samu da laifin kisan kai.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An yi wa wata matar aure da 'ya'yanta 6 kisan rashin Imani a Kano

Ya yi gargaɗin cewa duk gwamnan da ya ki ko ya jinkirta sanya hannu kan takardar aiwatar da hukuncin kisa ga wanda aka samu da laifi, alhakin wanda aka kashe yana kansa a ranar Al-kiyama.

Gwamna Abba ya magantu kan kisan Fatima

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna alhininsa kan kisan da aka yi wa wata matar aure da 'ya'yanta shida.

Gwamna Abba ya bayyana lamarin a matsayin mummunan aiki na rashin imani, marar dalili, kuma babban cin mutunci ga darajar ɗan Adam.

Hakazalika, Gwamna Abba ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan da abin ya shafa, mazauna Dorayi Chiranchi, da kuma al’ummar jihar Kano kan aukuwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng