Abu Ya Girma: An Fara Harbe Harbe da Masu Zanga Zanga Suka Tare Ministar Tinubu a Abuja
- Kananun 'yan kwangila sun fito zanga-zanga ranar Litinin a Abuja domin nuna fushinsu kan kudaden da gwamnatin tarayya ta rike masu
- Rahotanni sun nuna cewa masu zanga-zangar sun toshe kofar shiga ma'aikatar kudi, inda suka hana karamar ministar kudi shiga ofis
- Har yanzu dai ba a biya 'yan kwangilar hakkokinsu ba duk da matakan da Shugaba Tinubu da Majalisar Dattawa suka dauka a baya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Zanga-zangar da wasu 'yan kwangila suka fara ta dauki sabon salo a kofar ma'aikatar kudi ta Najeriya da ke babban birnin tarayya Abuja.
Masu zanga-zangar sun yi kicibus da Karamar ministar kudi, Doris Uzoka-Anite lokacin da fito da nufin shiga ofis yau Litinin, 19 ga watan Janairu, 2025.

Source: Twitter
Masu zanga-zanga sun tare Ministar kudi
Jaridar The Cable ta tattaro cewa masu zanga-zangar sun toshe tare da hana Ministar shiga ofis, lamarin da ya kara zafafa lamarin.
Masu zanga-zangar, karkashin kungiyar kananan ‘yan kwangila ta kasa (AICAN), sun toshe kofar ma’aikatar kudi ne saboda basussukan da suke bin gwamnatin tarayya.
Sa’ilin da Uzoka-Anite ta isa kofar shiga ma'aikatar, jami’an tsaro sun yi kokarin samar mata da hanya don ta shiga ciki, yunkurin da masu zanga-zangar suka bijirewa.
Jami'an tsaro sun yi harbe-harbe
Ana tsakiyar takaddamar, an ji karar harbe-harben bindiga yayin da jami’an tsaro suka yi kokarin tarwatsa masu zanga-zangar.
‘Yan kwangila sun zargi gwamnatin tarayya da kin biyan su kudaden ayyukan da suka riga suka kammala.
Haka kuma, sun zargi gwamnatin da kin sakin kudaden da aka ware musu a kasafin kudin shekarar 2024/2025.
A shekarar da ta gabata ma, ‘yan kwangilan sun gudanar da jerin zanga-zanga a harabar majalisar dokoki ta kasa da kuma ma’aikatar kudi.
Wane mataki gwamnatin tarayya ta dauka?
A watan Disambar 2025, Shugaba Bola Tinubu ya kafa wani kwamiti na ministoci daban-daban don magance matsalar basussukan da ake bin gwamnati, wadanda aka kiyasta sun kai kusan Naira tiriliyan 1.5.
Mambobin kwamitin sun hada da Ministan Kudi da Harkokin Tattalin Arziki, Wale Edun, da kuma Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Kaa, Atiku Abubakar Bagudu da Ministan Ayyuka, Dave Umahi.
Sauran sun hada da Ministan Harkokin Gudaje da Raya Birane, Ahmed Dangiwa, Darakta janar na ofishin kasafin kudi na tarayya, da kuma Zacch Adedeji, Shugaban hukumar tara kudaden shiga ta kasa (FIRS).

Source: Twitter
Haka zalika, wani kwamitin majalisar dattawa ya gayyaci Wale Edun don ya fito ya yi kararin bayani kan dalilan da suka janyo tsaikon biyan kudaden.
Sai dai duk da wadannan matakai, kananan yan kwangilan sun koka kan rashin biyansu hakkokinsu tare da fitowa zanga-zanga yau Litinin a Abuja, kamar yadda Leadership ta kawo.
An gano masu hannu a zanga-zangar Edo
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Monday Okpebholo, ya ce sun gano wadanda suka dauki nauyin zanga-zanga da ta barke a jihar Edo a ranar Asabar 11 ga watan Janairun 2026.
Monday Okpebholo ya tabbatar da cewa a binciken da aka yi, an gano masu daukar nauyin zanga-zangar da ta rikide zuwa tarzoma a Ekpoma.
A cewar Okpebholo, akwai manyan alamomi da ke nuna cewa ‘yan adawa, watakila da goyon bayan kasashen waje, suna daukar nauyin tayar da hankula.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

