ADC Ta Dauko Batun Zargin Ware Musulmi a Wata Yarjejeniyar Najeriya da Amurka

ADC Ta Dauko Batun Zargin Ware Musulmi a Wata Yarjejeniyar Najeriya da Amurka

  • Jam'iyyar ADC ta nuna damuwa kan yarjejeniyar da Najeriya ta rabbatawa hannu tsakaninta da Amurka don inganta harkar lafiya
  • ADC ta ce bayanan da gwamnatin Najeriya da Amurka suka gabatar sun banbanta, don haka akwai bukatar a fayyace wa jama'a ainihin gaskiya
  • A cewarta, Amurka ta nuna cewa yarjejenniyar za ta bai wa asibitocin kiristoci fifiko, wanda hakan ya saba wa kundin tsarin mulki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar ADC ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta fito ta yi karin haske yarjejeniyar hadin gwiwa kan harkar lafiya (MoU) da aka rattaba wa hannu kwanan nan tsakanin Najeriya da Amurka.

Jam’iyyar ADC ta dogara ne da yadda bayanan da gwamnatocin kasashen biyu suka bayar suka saba wa juna, musamman kan zargin nuna wariyar addini.

Kara karanta wannan

Yadda Amurka ta dogara da rahoton Inyamurin dan kasuwa aazaunin Onitsha wajen kai hari a Najeriya

Tambarin ADC.
Tambarin jam'iyyar hadaka, ADC Hoto: ADC Party
Source: Twitter

ADC ta gano matsala a yarjejeniyar Amurka

Tribune Nigeria ta tattaro cewa Najeriya ta bayyana yarjejeniyar a matsayin tsari na fasaha don karfafa fannin lafiya da fadada ayyukan kiwon lafiya na matakin farko.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi ya fitar ranar Lahadi, jam'iyyar ta lura cewa bayanan da gwamnatin Amurka ta fitar sun nuna cewa za a fifita asibitocin kiristoci a fadin Najeriya.

Ta ce hakan na iya saba wa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya kan nuna bambancin addini, sannan yarjejeniyar ta bai wa Amurka ikon dakatar da ita yadda ta ga dama, wanda hakan ya taba ikon Najeriya na cin gashin kanta.

Abin da ya sa ADC ta bukaci karin haske

A rahoton This Day, sanawar ta ce:

"Jam’iyyar ADC tana kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta fayyace abubuwan da ke cikin wannan yarjejeniya da kuma tasirinta, biyo bayan bayanan da suka saba wa juna da kasashen biyu suka fitar.

Kara karanta wannan

Harin Amurka: An 'gano' inda 'yan ta'adda ke tserewa saboda ruwan wuta a Sokoto

“Yayin da Gwamnatin Tarayya ta bayyana yarjejeniyar a matsayin tsarin karfafa fannin lafiya, bayanan da Amurka ta fitar sun nuna yarjejeniyar ta wata hanya daban.
"Bayanin Amurka ya nuna cewa za a karkatar da kudaden yarjejeniyar ne zuwa ga cibiyoyin lafiya da wani addini guda ke mara wa baya kawai.

ADC ta soki tsarin yarjejeniyar lafiya

ADC ta bayyana cewa bai kamata gwamnatin Najeriya ta shiga duk wata yarjejeniya da ke nuna bangaranci ko kuma wacce za ta cutar da kokarin dinkewar kasa da kundin tsarin mulki ya tabbatar ba.

"Abin mamaki ne yadda wadannan sharudda, da suka hada da bai wa Amurka ikon soke yarjejeniyar ita kadai, ba su fito a bayanin da gwamnatin Najeriya ta yi wa jama’a ba.
“ADC ta yi amanna cewa wannan bambancin bayani ba kuskure ba ne kawai; an yi hakan ne don kauce wa fushin jama'a, wanda hakan ya nuna akwai alamar tambayoyi kan gaskiya, bin tsarin mulki, da ikon Najeriya na cin gashin kanta.
"Ya kamata 'yan Najeriya su san wane nau'i na yarjejeniyar ne na gaske, da kuma dalilin da ya sa bayanin Abuja da na Washington suka bambanta haka," in ji sanarwar.

Kara karanta wannan

Bashir Ahmad ya soki Abba Kabir kan tsawaita maganar zuwa APC, ya fadi illar dambarwar

Shugaba Trump da Bola Tinubu.
Shugaban Amurka, Donald Trump da takwaransa na Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DonaldJTrump, @aonanuga1956
Source: Getty Images

ADC ta hango yadda za a ceto Najeriya

A baya, mun kawo rahoton cewa jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta koka kan salon mulkin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce babban manufar jam’iyyar adawar ita ce kifar da Shugaba Bola Tinubu daga mulki.

Bolaji Abdullahi ya bayyana hakan a matsayin wajibi domin ceto Najeriya daga abin da ya bayyana gazawa a fannin mulki da ba a taɓa ganin irinsa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262