'Wanda aka Kashe Matarsa da 'Ya'yansa 6 a Kano na Bukatar Taimako'
- Al’umma sun fara kira da a hada kai domin taimakawa mutumin da aka kashe 'ya'yansa shida da matarsa a Kano mai suna Malam Bashir Haruna
- Barista Abba Hikima ya bayyana jerin abubuwan da ya ce ya kamata a masa da nufin saukaka radadin da mutumin ke ciki tare da farfado da rayuwarsa
- Masu ruwa da tsaki sun bukaci gwamnati, attajirai da ’yan jarida su nuna tausayi a mu’amalarsu da wanda abin ya shafa lura da halin da yake ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano — Kisan gillar da aka yi wa 'ya'yan Malam Bashir Haruna shida tare da matarsa ya jefa al’umma cikin jimami, inda lamarin ya tayar da hankalin jama’a a fadin Kano da ma wajenta.
Bayan aukuwar wannan mummunan al’amari, mutane da dama sun fara kira da a hada karfi da karfe domin tallafa wa Malam Bashir, wanda aka bayyana a matsayin mutum da ya shiga wani mawuyacin hali maras misaltuwa.

Source: Facebook
Lauya mai kare hakkin dan Adam, Barista Abba Hikima na cikin wadanda suka fara kira kan a taimaka masa a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Taimakon wanda aka kashe iyalansa a Kano
Barista Abba Hikima ya fito fili ya yi kira ga shugabanni, attajirai da daukacin al’umma da su dauki nauyin taimakawa Malam Bashir Haruna.
Lauyan ya ce dole ne a yi rige-rige wajen canja rayuwarsa da yanayin mu’amalantarsa, domin kada ya ci gaba da rayuwa cikin tsananin damuwa da tunani.
A cewarsa, duk da cewa addu’a da neman hakkin jinini su ne manyan abubuwan da za su rage radadi, akwai bukatar daukar wasu matakai.
Daga cikin shawarwarin da ya bayar akwai taimaka masa yin Umra da Hajji domin samun nutsuwar rai, samar masa da jari mai karfi da zai ba shi damar rayuwa ba tare da fargabar yadda zai rayu ba.

Source: Facebook
Abba Hikima ya kara da cewa akwai bukatar sauya masa muhalli domin kada ya ci gaba da kallon wurin da aka yi wa iyalansa ta'addanci.
Ya kuma bukaci al’umma su yi duk abin da za su iya domin faranta masa rai, yana mai cewa hakan nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa.
Kira ga ’yan jarida da masu ziyara
Barista Abba Hikima ya ja kunnen ’yan jarida da sauran jama’a da ke yawan tambayar Malam Bashir yadda yake ji game da mutuwar iyalansa.
Ya ce irin wadannan tambayoyi na iya kara masa ciwo, yana mai cewa ko wane mai hankali ya san halin da mutumin ke ciki, don haka bai dace a matsa masa da tambayoyi masu kara tada masa hankali ba.
Shi ma Musbahu Baffa ya bayyana ra’ayinsa game da abin da ya faru da Malam Bashir Haruna a sakon da ya wallafa a Facebook.
Ya ce fuskarsa tana bayyana tsananin damuwa, karaya da bacin ran da ya mamaye zuciyarsa. A cewarsa, ko murmushi da za a gani a fuskar, wani yunkuri ne kawai na karfin hali.

Kara karanta wannan
"Ba za mu lamunta ba:" Gwamna Abba ya yi alkawarin nema wa fatima da yaranta adalci
Miji ya kashe matarsa a jihar Kebbi
A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta kama wani mutum da ake zargi ya kashe matarsa a cikin gidansu.
Rahotanni sun nuna cewa ana zargin cewa mijin ya yi amfani da fartanya wajen kisan matar bayan sabani ya shiga tsakaninsu.
Kakakin 'yan sanda ya tabbatar da kama mijin tare da cewa za a gurfanar da shi a gaban kotu da zarar hukumomi sun gama bincike.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

