Shugaba Tinubu Ya Aika Sako ga APC ta Kano kan Shirin Sauya Shekar Gwamna Abba

Shugaba Tinubu Ya Aika Sako ga APC ta Kano kan Shirin Sauya Shekar Gwamna Abba

  • 'Dan Majalisar wakilai daga Kano, Hon. Alhassan Ado Doguwa ya tabbatar da cewa an dakatar da shirin rijistar mambobin APC a jihar
  • A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Doguwa ya ce Shugaba Tinubu da APC ne suka dakatar da aikin
  • A cewarsa, Tinubu ya dauki wannan mataki ne saboda a jira Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kammala shiga APC don shi zai fara karbar katin zama mamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar da fara aikin rijistar mambobin jam’iyyar APC ta intanet a Jihar Kano.

Wannan umarni ya fito fili ne ta bakin ɗan Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, a cikin wani faifan bidiyo na daƙiƙu 27 da ke yawo a kafafen sada zumunta a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya turo sako daga kasar waje kan rasuwar malamin Musulunci a Najeriya

Alhassan Ado Doguwa.
Dan Majalisa mai wakiltar Doguwa da Tudun Wada, Hon. Alhassan Ado Doguwa Hoto: Alhassan Ado Doguwa
Source: Facebook

An dakatar da rijistar mambobin APC a Kano

A cikin bidiyon wanda jaridar Punch ta gani yau Lahadi, Doguwa ya bayyana cewa uwar jam'iyyar APC ta ƙasa, bisa umarnin Shugaba Tinubu, ce ta sanar da wannan mataki.

“Shugabancin jam’iyyar APC a matakin ƙasa, bisa umarnin Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya umarci a dakatar da fara rijistar mambobin APC a Kano,” in ji Doguwa.

Alhassan Ado Doguwa, wanda ke wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada a Majalisar Wakilai, na daga cikin manyan jiga-jigan APC a Kano.

Wannan mataki ya zo ne makonni kaɗan bayan Sakataren Yaɗa Labarai na APC a Kano, Ahmed Aruwa, ya sanar da cewa jam’iyyar na shirin fara rijistar 'ya'yanta.

Ahmed Aruwa ya bayyana cewa ana sa ran tsohon Gwamnan Kano kuma tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, zai halarci kaddamar fara wannan aiki.

Me yasa Tinubu ya dakatar da shirin?

Sai dai Hon. Doguwa ya nuna cewa wannan mataki na da alaka da shirin tarbar Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda zai sauya sheka zuwa APC.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi martani da dansa ya sauya sheka zuwa APC, zai goyi bayan tazarcen Tinubu

Abidiyon, wanda Liberal Radio ta wallafa a Facebook, Ado Doguwa ya ce:

“Me za ku yi idan Tinubu ya ce ya karɓiGwamna Abba? To, yau ya karɓe shi domin an shirya fara rijistar APC gobe, amma shugaban ƙasa da APC suka ce a dakata har sai Abba Kabir Yusuf ya koma APC a hukumance, domin shi ne zai fara karɓar katin zama mamba.”
Gwamna Abba Kabir.
Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnati Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Duk da cewa jam’iyyar APC ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba, wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin Gwamna Abba zai bar NNPP zuwa APC.

Tsawon makonni, wasu rahotanni sun nuna cewa an yi tattaunawar sirri tsakanin gwamnan, manyan jiga-jigan APC, da masu ruwa da tsaki a Abuja da Kano.

Gwamna Abba ya gabatar da bukata ga APC

A wani rahoton, kun ji cewa shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na sauya sheka daga NNPP zuwa APC ya samu tangarda kan bukatar tikitin takara a 2027.

Kara karanta wannan

Zafin siyasa bai hana aiki: Abba ya fadi shirin gwamnati a kan matasa 50, 000 a Kano

Wasu majiyoyi sun ce an samu jinkiri nr sakamakon rashin amincewar APC da bukatar Gwamna Abba, wanda ya nemi tikitin takara kai tsaye a zaben gwamna na 2027.

Rahotanni sun nuna cewa bukatar tikitin kai tsaye na daga cikin sharudan da Gwamna Yusuf ya gindaya wa shugabancin APC kafin.sauya shekarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262