Sojojin Saman Najeriya Sun Yi Ruwan Bama Bamai a Borno, Mutane fiye da 40 Sun Mutu
- Rundunar sojojin saman Najeriya ta samu nasarar hallaka 'yan ta'adda fiye da 40 a yankunan Azir da Musarram na Jihar Borno
- Air Marshal Sunday Aneke ya ce hadin gwiwa tsakanin dakarun sama da na kasa ya taimaka kwarai wajen tarwatsa 'yan ta'adda
- An kai wannan farmaki ne matsayin daukar fansa da kuma dakile hare-haren yan ta'adda a ddade suna addabar garuruwan Borno
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Rundunar sojojin saman Najeriya ta sanar da kakkabe yan ta’adda fiye da 40 a wasu jerin hare-hare na hadin gwiwa da aka kai a yankunan Azir da Musarram na Jihar Borno.
Wannan nasara tana kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama'a na rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar ranar Lahadi a birnin Abuja.

Source: Twitter
Yadda sojoji suka kai samame yankin Azir
Ejodame ya bayyana cewa an gudanar da wadannan hare-hare ne a ranakun 15 da 16 ga Janairu, 2026, karkashin rundunar hadin gwiwa ta Operation HADIN KAI, in ji rahoton Punch.
A daren 16 ga Janairu, jiragen yakin rundunar sun kai dauki cikin gaggawa bayan samun kiran gaggawa daga yankin Azir inda sojoji ke fafatawa da maharan.
Binciken na’urori ya nuna cewa yan ta’addan na kokarin sake haduwa a karkashin bishiyoyi, lamarin da ya sa jiragen yakin suka saki bama-bamai a kansu.
Sanarwar ta ce:
"Binciken da aka gudanar bayan harin ya tabbatar da cewa babu sauran barazana a yankin, sannan bayanan mazauna yankin sun nuna lamura sun daidaita yanzu."
Tarwatsa taron yan ta’adda a Musarram
A ranar 15 ga Janairu, 2025, rundunar ta kai wani harin ba-zata a yankin Musarram dake cikin Tumbuns bayan samun bayanan sirri kan taron yan ta'adda a cikin kwalekwale.
Jiragen yakin sun hangi kwalekwale kusan 10 dauke da 'yan ta’adda fiye da 40 wadanda ke shirin kai hari a yankunan Baga da kuma madatsar ruwa ta kifi.
Jaridar Vanguard ta rahoto Ejodame ya kara da cewa:
"Mun bi sawun wadanda suka yi kokarin tserewa muka kakkabe su, sannan muka tarwatsa duk wani taro na yan ta'adda a yankin."
Alƙawarin shugaban dakarun sojin sama
Shugaban dakarun sojin saman Najeriya, Air Marshal Sunday Aneke, ya jaddada aniyar rundunarsa na ci gaba da ba da tallafi ga dakarun kasa domin fatattakar dukkan yan ta'adda.
Aneke ya ce:
"Wadannan ayyuka sun nuna tasirin yin amfani da bayanan sirri da kuma hadin gwiwa tsakanin dakarun sama da na kasa wajen dakile ayyukan yan ta'adda."
Ya tabbatar wa yan Najeriya cewa rundunar za ta ci gaba da matsa lamba har sai an kakkabe yan ta’adda tare da dawo da zaman lafiya a yankunan.
'Yan ta'adda sun kashe Janar Uba
A wani labari, mun ruwaito cewa, Janar Musa Uba, Kwamandan Runduna na Damboa, ya rasu bayan harin da mayaƙan ISWAP suka kai a yankin Azir Multe.
Labarin ya girgiza mutane da dama, musanman ganin girman jami'in sojin da yadda aka samu labarin cewa ya fadawa sojoji dai dai inda yake, a hanyar komawa barikinsu.
Dakarun ƙasa da na sama sun yi ƙoƙarin ceto shi, amma an sake kama shi bayan rahoton cewa an sace shi ya yadu a kafafen yada labarai.
Asali: Legit.ng


