Hare-hare biyar na makiyaya da suka dimauta 'yan Najeriya

Hare-hare biyar na makiyaya da suka dimauta 'yan Najeriya

Legit.ng da sanadin jaridar The Punch ta kawo muku jerin hare-hare biyar na makiyaya da afku a yankunan Arewacin kasar nan, wadanda suke jefa firgici tare da dimaucewa a zakutan al'ummar Najeriya a sakamakon muninsu.

A halin yanzu batutuwa rikicin makiyaya da manoma na ci gaba da gudana akan harsunan al'ummar kasar nan, kama daga cin zarafi, keta haddi, asarar dukiya da kuma rayuka da hare-haren ya janyo a kasar nan.

Hare-hare biyar na makiyaya da suka dimauta 'yan Najeriya
Hare-hare biyar na makiyaya da suka dimauta 'yan Najeriya

Ga jerin hare-hare biyar mafi muni da makiyaya suka yi sanadi a fadin kasar nan:

1. Garkuwa tare da neman kudin fansar tsohon ministan kudi na Najeriya, Samuel Oluyemisi Falae, wanda yafi shahara da sunan Olu Falae.

Makiyaya bakwai sun kai hari gonar tsohon ministan a ranar 21 ga watan Satumba na shekarar 2015, inda suka yi gaba dashi domin azabtarwa tare da neman kudin fansa har na wuri na gugar wuri na N100m.

2. Harin ranar 20 ga watan Nuwamban 2017, inda makiyaya suka kai hari kan al'ummar Numan dake jihar Adamawa wanda rahotanni suka bayyana cewa anyi asarar rayuka kimanin 30 zuwa 50.

3. Harin ranar 1 ga watan Janairun sabuwar shekarar 2018 a jihar Benue, inda ya salwantar da rayuka 50 tare da raunatar fiye da mutane 100. Wannan harin ne ya sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci sufeto janar na 'yan sanda, Ibrahim Idris ya tattara ina-sa-ina-sa zuwa jihar domin fuskantar matsalar.

KARANTA KUMA: Baƙin haure 200 sun dilmeyi yayin ketare tekun bahar Maliya

4. Harin ranar 6 ga watan Janairun 2018 akan al'ummar garin Lau dake jihar Taraba wanda adadin rayukan da suka salwanta sun haura 50.

5. A watan Agustan shekarar da ta gabata, makiyaya biyu suka yi rubdugu wajen fyade wata dattijuwa mai shekaru 72 a duniya. Victoria Akinseye wadda mazauniyar karamar hukumar Ore ce a jihar Ondo, ta fada hannun 'yan ta'addan ne a yayin da take gudanar da 'yan aikace-aikace a gonar ta.

A watan Oktoban shekarar da ta gabata dai, wasu makiyaya biyu sun fyade wata budurwa 'yar shekaru 14 a unguwar Tudun Lambaga dake karamar hukumar Eggon a jihar Nasarrawa.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng