Magana Ta Fito: An Ji Abin da Ya Jawo Jinkiri game da zuwan Abba Kabir APC

Magana Ta Fito: An Ji Abin da Ya Jawo Jinkiri game da zuwan Abba Kabir APC

  • Shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na sauya sheka daga NNPP zuwa APC ya samu tangarda kan bukatar tikitin takara a 2027
  • Shugabannin APC sun ki amincewa da bukatar da aka ce gwamnan ya nema suna nacewa cewa dole gwamnan ya bi tsari
  • Rikicin sauya shekar na kara tayar da jijiyoyin wuya a Kano, yayin da APC ke cewa gwamnan zai shiga jam’iyyar “a lokacin da ya dace”

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Shirin sauya shekar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, daga jam’iyyar NNPP zuwa APC ya samu tsaiko.

Wasu majiyoyi sun ce hakan ya faru ne sakamakon rashin amincewar APC da bukatar tikitin takara kai tsaye a zaben gwamna na 2027.

An samu tsaiko game da sauya shekar Abba Kabir zuwa APC
Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da Gwamna Abba Kabir. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

An 'gano' abin da ya hana Abba zuwa APC

Rahotanni sun nuna cewa bukatar tikitin kai tsaye na daga cikin sharudan da Gwamna Yusuf ya gindaya wa shugabancin APC kafin sauya shekarsa zuwa jam’iyyar mai mulki, cewar ThisDay.

Kara karanta wannan

Bashir Ahmad ya soki Abba Kabir kan tsawaita maganar zuwa APC, ya fadi illar dambarwar

Sai dai shugabannin APC sun nuna rashin shirin sadaukar da tsarin jam’iyya saboda sauya shekar gwamnan.

Wata majiya ta bayyana cewa kin amincewar APC da bukatar ya janyo fargaba a sansanin gwamnan, lamarin da ya sa aka dage sauya shekar fiye da sau daya a baya.

Ana kuma cewa bukatar gwamnan ta ci karo da muradin wasu manyan ’yan APC a Kano, ciki har da Sanata Barau Jibrin, wanda ake cewa yana da burin tsayawa takarar gwamna a 2027.

Wata majiya kusa da tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje, ta ce jam’iyyar ba za ta sadaukar da burin shugabanninta na kasa saboda sauya shekar Gwamna Yusuf ba.

Baya ga tikitin kai tsaye, rahotanni sun ce gwamnan na bukatar ikon nada minista daga Kano da kuma bai wa magoya bayansa mukaman tarayya, ciki har da wadanda ’yan APC ke rike da su a yanzu.

Ana ci gaba da dambarwa kan komawar Abba zuwa APC
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Matsayarwasu yan APC kan zuwan Abba Kabir

Sai dai APC na nacewa cewa duk masu sha’awar takarar gwamna, ciki har da Gwamna Yusuf, dole su shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Sauya sheka: Wasu 'yan APC na maganar hana Abba takara a 2027

A halin da ake ciki, mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da zama a NNPP, lamarin da ka iya haddasa rikici ko barazanar tsige gwamnan idan ya sauya sheka.

Har ila yau, alamun cewa sauya shekar ba ta kammala ba sun kara bayyana lokacin da Gwamna Abba Kabir ya jagoranci taron majalisar zartarwa ta jiha a Abuja, inda ya bayyana sanye da hular ja ta Kwankwasiyya tare da tutar NNPP a bayyane.

Abin da APC ta ce kan jita-jitar

Sai dai APC a Kano ta ce Gwamna Yusuf na kan hanyarsa ta shiga jam’iyyar, inda ta karyata rade-radin cewa an taba ganawa da shi kan tikitin takara kai tsaye.

Sakataren APC a Kano, Alhaji Zakari Sarina, ya ce jam’iyyar na maraba da gwamnan a kowane lokaci, yana mai kira ga jama’a da su yi watsi da jita-jita, cewar Arise News.

NNPP ta shawarci Abba Kabir kan sauya sheka

Mun ba ku labarin cewa jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa har yanzu tana fatan Gwamna Abba Kabir Yusuf zai dakatar da shirin sauya sheka zuwa APC.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, an gano dalilai 3 da suka jawo jinkirin sauya shekar Gwamna Abba zuwa APC

Kakakin jam’iyyar ya ce gudanar da tattaunawa da shawarwari a kan matsalar, kuma lokaci bai kure ba kan batun yanke hukunci.

Ladipo Johnson ya bukaci ‘yan Kwankwasiyya su guji duk wani kazamin rikici, tare da kiyaye hadin kai da fahimtar juna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.