"Ba za Mu Lamunta ba:" Gwamna Abba Ya Yi Alkawarin Nema wa Fatima da Yaranta Adalci

"Ba za Mu Lamunta ba:" Gwamna Abba Ya Yi Alkawarin Nema wa Fatima da Yaranta Adalci

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nuna alhini a kan kisan gilla da wasu miyagu suka yi wa sata uwa da ’ya’yanta a Dorayi Chiranchi
  • Ya bayyana cewa ba za a lamunci irin wannan ta'addanci ba, saboda haka ha ba ’yan sanda umarnin kamo mutane
  • Gwamnati ta umarci ƴan sintiri da su ƙarfafa sintiri da tsaron al’umma domin hana faruwar irin wannan lamari a gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matuƙar baƙin ciki da alhini kan kisan gilla da aka yi wa wata mata ’yar Kano, Fatima Abubakar tare da ’ya’yanta a unguwar Dorayi Chiranchi.

Gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin mummunan aiki na rashin imani, marar dalili, kuma babban cin mutunci ga darajar ɗan Adam.

Kara karanta wannan

ADC: Momodu ya kare Atiku kan zargin shirin amfani da kuɗi wajen sayen takara

Gwamnan Kano ya yi takaicin kashe Fatima da yaranta
Yaran Fatima 6 da aka kashe a Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Isa Ibrahim Suleiman/Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Asabar bayan da rasuwar bayin Allah.

A cewar sanarwar da Sanusi Bature ya wallafa a shafin Facebook, Gwamna ya ce ba za a taɓa amincewa da irin wannan cin mutuncin rayuwar ɗan adam ba.

Abba ya yi ta'aziyyar kashe uwa da yaranta

Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan da abin ya shafa, mazauna Dorayi Chiranchi, da kuma al’ummar Jihar Kano baki ɗaya bisa wannan rashin imani.

Ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya jiƙan waɗanda suka rasu, Ya gafarta masu, Ya ba su Aljannar Firdausi, tare da ba iyalansu haƙurin jure wannan mummunan rashi

A kalamansa, Gwamna Abba ya jaddada cewa gwamnatin sa ba za ta lamunci aikata laifuffuka masu tayar da hankali ba.

Ya Kafa fa cewa za a bi dukkanin hanyoyin doka domin ganin an hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan aika-aika.

Kara karanta wannan

Zafin siyasa bai hana aiki: Abba ya fadi shirin gwamnati a kan matasa 50, 000 a Kano

Gwamnan Kano ya ba yan sanda umarni

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarni kai tsaye ga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano da ta tashi tsaye wajen farautar duk masu hannu a kisan, tare da tabbatar da an kamo su an kuma gurfanar da su gaban kotu.

Gwamnan Kano ya ce za a tabbatar an yi wa Fatima da yaranta adalci
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Ya yi gargaɗi cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada ba tare da rangwame ko da ƙalilan ba.

Baya ga haka, gwamnan ya umarci Hukumar tsaron jihar ta Kano 'Neighborhood Corps' da ta ƙara yawan sintiri da sa ido a unguwanni masu rauni, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin da gwamnatin ke yi na ƙarfafa tsaro.

Gwamna Abba ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu, su ba hukumomin tsaro cikakken haɗin kai, tare da rika sanar da duk wani motsi ko abu da suka ga yana da alamar barazana.

Ya tabbatar da cewa gwamnatin Jihar Kano ta jajirce wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, kuma ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen samar da zaman lafiya da tsaro ga kowa.

Kara karanta wannan

Ana shirin sakin ƴan ta'adda 70, sun laftawa manoma a Kano da Katsina haraji

An kashe uwa da yaranta a Kano

A wani labarin, kun ji cewa mutanen Chiranci da ke jihar Kano sun yuni a cikin tashin hankali bayan wasu mutane sun haura gidan matar aure mai suna Fatima, suka kashe ta da yaranta shida.

Mazauna yankin sun bayyana lamarin a matsayin abin firgici da ban tsoro, wanda ba a taɓa ganin irinsa ba, inda suka nuna alhini da fargaba kan asarar rayukan bayin Allah da aka yi a ranar Asabar 17 ga watan Janairu, 2026.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara yawan sintiri a yankin tare da tabbatar da cewa an kama waɗanda suka aikata laifin domin su fuskanci hukunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng