Lamari Ya Girma: Mata Sun Yi Wa Gwamna Barazana, Za Su Yi Tsirara a Zanga Zanga

Lamari Ya Girma: Mata Sun Yi Wa Gwamna Barazana, Za Su Yi Tsirara a Zanga Zanga

  • Tashin hankali ya barke a yankin Ekid, Akwa Ibom, bayan kama wata mai fafutukar nemawa al'umma yanci
  • An kama matar ce mai suna Princess God’sown Udoito wacce ke sukar Gwamna Umo Eno kan batun filaye da muhalli
  • Kungiyar 'Ekid Women Wing' ta yi barazanar zanga-zanga da kaurace wa ayyukan gwamnati, tana zarginta da murkushe ‘yancin fadin albarkacin baki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Uyo, Akwa Ibom - Tashin hankali ya ci gaba da mamaye al’ummar yankin Ekid a jihar Akwa Ibom, biyo bayan kama Princess God’sown Udoito.

Udoito fitacciyar ‘yar gwagwarmayar kare filaye da muhalli wacce ta yi kaurin suna wurin sukar Gwamna Umo Eno.

Mata za su fito zanga-zanga tsirara
Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom. Hoto: Pastor Umo Eno.
Source: Facebook

Rigima ta barke kan cafke yar gwagwarmaya

Rahoton Leadership ya ce an kama Lady Udoito ne bisa umarnin gwamnatin jihar, sannan aka gurfanar da ita a kotu kan zargin bata suna da tayar da hankalin jama’a.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗan kasar waje a Najeriya bayan hallaka ɗan sanda

Kungiyar 'Ekid Women Wing', wacce ta kunshi mata daga Eket da Esit Eket, ta yi Allah-wadai da abin da ta kira danniya karkashin mulkin Gwamna Umo Eno.

Matan sun ce sun yanke shawarar kaurace wa dukkan harkokin siyasa har sai an saki Princess Udoito daga gidan yari ba tare da wani sharadi ba.

Sun bayyana cewa an kama ta ne saboda ta soki shirin sayar da dajin Stubbs Creek, filin gadon Ekid, ba tare da amincewar al’ummar yankin ba.

Daya daga cikin shugabannin mata, Ekaette Bassey, ta ce an riga an shirya zanga-zanga, tare da barazanar janye goyon baya ga tazarcen gwamnan.

Matan sun gargadi cewa idan ba a saki Udoito cikin mako guda ba, za su tsaurara zanga-zanga har da fitowa tsirara domin nuna adawa.

Mata sun yi barazanar yin zanga-zanga tsirara a Akwa Ibom
Taswirar jihar Akwa Ibom a Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Zargin da ake yi wa Gwamna Eno

Sun zargi gwamnan da amfani da tsoratarwa domin hana su fadin albarkacin baki, suna mai cewa ba za su ja da baya ba wajen kare hakkokinsu, cewar Vanguard.

Ta ce:

“Mun yi Allah-wadai da matakin Gwamnan, kuma muna roƙonsa ya saki Princess Udoito, ba tare da wani sharadi ba.

Kara karanta wannan

An kori Sarki daga fadarsa, Gwamna zai sanya masa ido bayan dakatar da shi

"Idan ya gaza yin hakan, ba za mu da wata mafita illa fitowa tsirara tare da mamaye otal dinsa da ke kan titin Eket–Oron yayin zanga-zanga.
“Sanya takunkumi ga ‘yancin fadin albarkacin bakinmu alama ce cewa Gwamna Eno ba ya son goyon bayanmu, kuma ba za mu nuna tsoro ko ja da baya ba."

Wannan lamari ya fara dagula lamura a yankin yayin ake ci gaba da fargabar komai na iya faruwa da kuma barazanar tsaro a wurin.

Akwa Ibom: Majalisa ta musanta shirin hana zina

Mun ba ku labarin cewa yan majalisar dokokin Akwa Ibom sun yi magana kan jita-jitar za su kawo kudirin haramta zinace-zinace a jihar.

Majalisar ta yi gaggawar karyata rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa tana duba kudirin dokar domin amfani da ita.

Rahoton ya yi ikirarin cewa an tanadi hukunci ga mata marasa aure, yayin da mazan aure za su biya tarar miliyoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.