Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Ɗan Kasar Waje a Najeriya bayan Hallaka Ɗan Sanda

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Ɗan Kasar Waje a Najeriya bayan Hallaka Ɗan Sanda

  • Mutane sun shiga tashin hankali da yan bindiga suka kai hari a cikin gona inda suka hallaka jami'in dan sanda da ke gadinta
  • An kai harin ne a gonar Aqua Triton a Ogunmakin, Ibadan da ke jihar Oyo inda suka sace wani ɗan ƙasar waje
  • Marigayi dan sandan mai suna Imoobe Prester, ya yi artabu da ’yan bindigar domin hana satar, amma aka harbe shi har lahira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Wasu mutane dauke da muggan makamai da ake zargin yan bindiga ne sun kai hari a cikin gona.

'Yan sanda sun ce ’yan bindigar sun sace wani ɗan India tare da kashe jami’in tsaro a wani hari da suka kai.

An kashe dan sanda a harin yan bindiga a Oyo
Sufeta-Janar na yan sanda, Kayode Egbetokun. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa harin ya faru ne a gonar Ogunmakin a Ibadan da ke Jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Ana fargabar harin Bello Turji, 'yan bindiga sun yi ta'asa a Sokoto

An rasa rayuka bayan harin yan bindiga

Jihar Oyo na daga jihohin da ke fama da hare-haren yan bindiga wanda ke jawo asarar rayuka da duniyoyin al'umma.

Ko a kwanan ma, 'yan bindiga sun kai mummunan farmaki gandun dabbobin daji na gwamnatin tarayya a jihar Oyo, suka kashe jami'an tsaron wurin da dama.

Bayanai sun ce maharan sun bude wa jami'an NPS, masu a'hakin tsare gandun dabbobi wuta a harin da suka kai cikin dare.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da tura jami'an tsaro domin tabbatar da tsaro da dawo da doka da oda.

Yadda aka sace dan kasar India a Oyo

Rahotanni sun nuna cewa an sace dan India ne ranar 16 ga Janairun 2026 da misalin karfe 1:00 na rana.

An sace mutumin ne a gonar kamfanin Aqua Triton, inda ’yan bindiga kusan 10 suka kai hari.

An ce ’yan bindigar sun sace Renjith Pillai mai shekaru 42, daraktan kamfani, a lokacin da yake duba amfani a gonar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ƴan bindiga sun kai mummunan hari kan ƴan sanda, an rasa rayuka

Yan bindiga sun sace dan India a Oyo
Taswirar jihar Oyo da PDP ke mulki a Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda dan sanda ya gwabza da yan bindiga

Rahoton ya ce jami’an PMF hudu ne ke bakin aiki a gonar, inda Sufeta Imoobe Prester ya yi artabu da ’yan bindigar domin hana satar.

A yayin musayar wuta, ’yan bindigar sun harbe shi suka kwace bindigarsa kirar AK-47, sannan suka tsere da ɗan India.

An garzaya da jami’in asibiti domin jinya, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa sakamakon harbin da aka yi masa.

Rundunar tsaro ta haɗa jami’an ’yan sanda, PMF, sashen yaki da garkuwa, mafarauta da ’yan sa-kai domin bin diddigin ’yan bindigar.

An ajiye gawar marigayin a dakin ajiye gawarwaki na Asibitin Adeoyo da ke kan hanyar Ring Road, Ibadan, yayin da bincike kan lamarin ke ci gaba.

Yan sanda suna binciken barazanar ƴan bindiga

Kun ji cewa rundunar ‘yan sandan Oyo ta fara bincike bayan gano wasiƙun barazana daga ‘yan bindiga zuwa ga al'umma.

Kara karanta wannan

Neman sulhu: Ƴan bindiga sun gindaya wa gwamnatin Katsina sharudda 8 masu tsauri

An ce wasiƙun biyu sun haddasa fargaba, inda ɗaya ke cikin harshen Yarbanci, ɗaya kuma Turanci suna barazanar hari ranar 20 ga Janairu, 2026.

'Yan sanda sun bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu, suna cewa ana gudanar da bincike mai zurfi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.