Ta’addanci: Yan Bindida 80 Sun Mika Wuya, Gwamnati Ta Gindaya Sharuda

Ta’addanci: Yan Bindida 80 Sun Mika Wuya, Gwamnati Ta Gindaya Sharuda

  • Fiye da ’yan bindiga 80 sun ajiye makamansu da kansu tare da rungumar shirin sulhu da sake tsugunarwa na gwamnati
  • Rahotanni sun nuna cewa matsin lambar sojoji da tattaunawa da shugabannin al’umma sun tilasta rushe sansanonin ’yan bindiga biyu
  • Gwamnati ta bayyana mika wuya da aka yi a matsayin babban ci gaba wajen dakile ta’addanci da laifukan teku a kudancin Cross River

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Calabar, Cross River - Akalla ’yan bindiga 80 da ke aiki a gabar ruwa ta karamar hukumar Akpabuyo a Jihar Cross River suka ajiye makamansu da kansu.

Tsofaffin yan tawayen sun ajiye makaman tare da amincewa da shirin sulhu da sake tabbatar da samun zaman lafiya a fadin jihar.

Yan bindiga sun mika makamansu a Cross River
Yan bindiga da suka mika makamansu a Cross River. Hoto: @ZagazOlamakama.
Source: Twitter

Yan bindiga sun ajiye makamansu a Cross River

Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da haka a shafin X inda ya ce ’yan bindigar sun fito da yawa daga maboyarsu a yankin Atimbo, karkashin Operation OKWOK.

Kara karanta wannan

Soja ya samu rauni da gobara ta kama gidan sojoji, ta kona masallacinsu a Yobe

Yankin na daga cikin yankin da Rundunar Sojin Najeriya ta Brigade ta 13 ke kula da shi a fadin jihar.

Rahotanni sun bayyana hakan a matsayin gagarumin ci gaba a yaki da ta’addanci da laifukan teku a kudancin Cross River.

Majiyoyin tsaro sun shaida cewa mika wuya da aka samu sakamakon matsin lambar sojoji na tsawon watanni ne, tare da tattaunawa a boye da shugabannin al’umma, jami’an gwamnati da hukumomin tsaro.

Yan bindiga sun bukaci sulhu da gwamnati
Taswirar jihar Cross River da yan bindiga suka mika makamansu. Hoto: Legit.
Source: Original

Sansanonin yan bindiga da suka mika wuya

An bayyana cewa sansanonin ’yan bindiga biyu ne suka mika kansu a lokaci guda inda sansani na farko, karkashin jagorancin ThankGod Ebikontei, wanda aka fi sani da Ayibanuagha, ya gabatar da mayaka 39.

Duk da haka, ana sa ran wasu hudu za su mika wuya nan gaba domin tabbatar da samun lafiya a yankin da ke fama da matsalar tsaro.

Sansani na biyu kuma, wanda John Isaac, wanda ake kira Akpokolo, ke jagoranta, ya fito da mayaka 41 domin nuna shirinsu game da shirin, cewar BBC Hausa.

Kara karanta wannan

Musulunci ya yi rashi: 'Yan bindiga sun hallaka malamin addini a Kaduna

Wannan kungiyar da aka fi sani da 'Akpokolo Marine Forces' ko “Border Boys” ta dade tana iko da manyan hanyoyin ruwa da ya hada Cross River da sauran yankunan bakin teku.

Rahotanni sun ce ana sa ran karin yan bindiga 10 daga kungiyar Akpokolo za su shiga shirin afuwa.

Gaba daya, ’yan bindiga 80 sun fice daga dazuka da gabar ruwa zuwa shirin kwance damara da gyara rayuwa karkashin kulawar gwamnati.

Yan bindiga sun nemi sulhu a Kogi

Mun ba ku labarin cewa gwamnatin Kogi ta ce matsin lamba da ruwan wuta daga jami’an tsaro ya tilasta wa wasu ’yan bindiga neman sulhu da mika makamansu.

Mai bai wa gwamna shawara kan tsaro ya ce amfani da fasaha da kayan aiki ya raunana ’yan ta’adda sosai wanda ya tilasta su neman zaman sulhu.

Gwamnati ta jaddada matsayarta game da tattaunawa da ’yan bindiga ba, tana shirin kafa doka da za ta haramta zama a daji a fadin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.