Jirgin Qatar Airways Dauke da Mutane 260 Ya Gamu da Matsala bayan Tashinsa a Najeriya
- Wani jirgin sama mallakin kamfanin sufuri na Qatar Airways ya yi saukar gaggawa jim kadan bayan tashinsa a jihar Legas
- Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya gamu da tangardar na'aura jim kadan bayan ya lula sama, lamarin da ya tilasta komawarsa filin jirgi
- Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas ta tabbatar da aukiwar lamarin, inda ta ce babu wanda ya samu rauni daga cikin fasinjoji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Wani jirgin Qatar Airways ya gamu tangardar na'ura jim kadan bayan tashinsa daga Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed (MMIA), da ke Legas a daren Juma’a.
Rahotanni sun nuna cewa jirgin saman ya yi gaggawar komawa filin jirgin Legas bayan samun matsalar, domin ceton fasinjojin da ya dauka.

Source: Original
Abin da ya faru bayan tashin jirgi a Legas
Majiyoyi sun shaida wa wakilin Daily Trust cewa matukin jirgin ya sanar da masu kula da zirga-zirgar jiragen sama (ATC) game da wata matsalar injina bayan ‘yan mintuna da tashinsa.
Matukin ya kuma nemi izinin dawowa cikin gaggawa kuma aka amince masa, lamarin fa ya sa jirgin ya koma filin jirgin saman NMIA nan take.
Jirgin na ɗauke da mutane 260, ciki har da fasinjoji 248 da ma’aikata 12. Kamfanin Qatar Airways na amfani da jiragen Boeing 787-800 da 787-900 a zirga-zirgarsa tsakanin Doha da Lagos.
Har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da ainihin matsalar na'urar da aka samu ba.
Hukumar NCAA ta tabbatar da hatsarin
Sai dai Daraktan Hulɗa da Jama’a da Kare Haƙƙin Fasinjoji n koa Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA), Mista Michael Achimugu, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce:
“Zan iya tabbatar da cewa jirgin saman ya yi komawar gaggawa. Za a fitar da ƙarin bayani daga baya.”
Haka kuma, wata majiya daga Hukumar Binciken Harkokin Jiragen Sama ta Najeriya (NSIB) ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana shi a matsayin babban lamari mai hatsari.

Kara karanta wannan
Jigon ADC ya zargi Tinubu da sakaci, an tsunduma mutane miliyan 141 a bakin talauci
Sai dai zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, hukumar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Fasinjojin jirgin sun samu rauni?
A gefe guda, Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Lagos (LASEMA) ta ce ta karɓi kiran neman taimako ta layukanta guda biyu, 767 da 112 dangane da jirgin.
A cikin wata sanarwa da Darakta Janar na LASEMA, Dr. Olufemi Oke-Osanyintolu, ya sanya wa hannu, ya ce an tura tawagar ba da agaji nan take zuwa filin jirgin sama.

Source: Getty Images
A cewar LASEMA, binciken farko ya nuna cewa jirgin ya fuskanci matsalar fasaha yayin da ya tashi zuwa sararin samaniya, wanda hakan ya sa aka yi saukar gaggawa a Lagos.
An fitar da dukkan fasinjojin lafiya, kuma ba a samu wani rauni ba. Haka kuma, hukumar ta ce jirgin bai samu mummunar lalacewa ba sakamakon lamarin.
An karkatar da jirgin Kano zuwa Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa wasu musulmai da suka dawo daga Umrah a Saudiyya su gamu da tangarda yayin da jirgin da ya dauko su zai sauka a jihar Kano.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun ci gaba da ta'asa a Benue, an hallaka dan sanda da jikkata matafiya
Rahoto ya nuna cewa rashin kyaun yanayi ya sa aka karkata da akalar jirgin sama zuwa Abuja maimakon sauka a Kano kamar yadda aka tsara masa.
Wasu daga cikin fasinjojin sun koka cewa an barsu a cikin jirgin ba tare da abinci, ruwa, ko cikakken bayani daga kamfanin jirgin ba na tsawon awanni.
Asali: Legit.ng
