Bam Ya Tarwatse da Matafiya a Zamfara, Ya Yi Barna Mai Girma

Bam Ya Tarwatse da Matafiya a Zamfara, Ya Yi Barna Mai Girma

  • Wani abin fashewa da ake zargin bam ne da 'yan bindiga suka dasa ya tashi da matafiya a jihar Zamfara
  • Lamarin ya auku ne lokacin da mutanen suke tsaka da tafiya a kan hanya, kwatsam kawai sai suka taka bam din da aka dasa
  • Fashewar bam din ta jawo jami'an tsaro sun takaita zirga-zirga a kan hanyar yayin da suke ci gaba da kokarin dakile duk wata barazana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Matafiya biyar sun jikkata bayan da wani abin fashewa (IED) ya tashi da su a jihar Zamfara.

Lamarin ya auku ne a kan hanyar Takalafiya–Gadar Zaima da ke karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara.

Matafiya sun jikkata bayan dasa bam a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda gobara ta tashi ana tsakiyar sauke fetur a wani gidan mai a Kano

Matafiya sun taka bam a Zamfara

Fashewar ta faru ne da misalin karfe 11:30 na safe a ranar Alhamis, 15 ga watan Janairun 2026 lokacin da babur ɗauke da fasinjoji biyar ya taka kan bam ɗin da ake zargin ’yan bindiga ne suka dasa.

Ana zargin 'yan bindiga ne suka dasa bam din da nufin kai hari kan jami’an tsaro da ke sintiri a yankin da ke fama da rikici.

Fashewar ta lalata babur ɗin gaba ɗaya tare da jikkata dukkan fasinjojin biyar da ke kansa.

Wane mataki jami'an tsaro suka dauka?

Nan take jami’an tsaro suka rufe hanyar domin hana zirga-zirgar ababen hawa, tare da gargaɗin mazauna yankin da su guji kusantar wajen, yayin da ake gudanar da bincike domin gano ko akwai wata barazana a yankin.

Daga bisani an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa babban asibitin Gummi domin samun kulawar likita.

An takaita zirga-zirga a kan hanyar Takalafiya–Gadar Zaima, yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da sa ido da kuma tabbatar da cewa hanyar ta kuɓuta daga duk wata barazana da ka iya tasowa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ci gaba da ta'asa a Benue, an hallaka dan sanda da jikkata matafiya

'Yan bindiga sun dasa bam a Zamfara
Jami'an 'yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Ana dasa bama-bamai a Zamfara

Jaridar The Cable ta ce a watan Disamba na shekarar 2025, wasu matafiya da ke bin hanyar Gurusu–Gwashi a karamar hukumar Bukkuyum sun jikkata tashin wani bam da ake zargin ’yan bindiga ne suka dasa shi.

Kwanaki kaɗan bayan haka kuma, an ruwaito cewa aƙalla mutane tara sun mutu bayan da wasu bama-bamai guda biyu suka tashi a kan hanyar Magami–Dansadau da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

An ce ’yan bindiga ne suka dasa bama-baman a kan hanyar da ke tsakanin al’ummomin Maikogo da Mai’ayaya.

'Yan bindiga sun kashe mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan wani kauye a jihar Sokoto.

Tsagerun 'yan bindigan sun dira kauyen da sanyin safiya inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi, lamari da ya jawo asarar rayuka tare da raunata wasu mutane.

'Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da mutanen da ba a san adadinsu ba, a harin wanda suka kai a wani kauye na karamar hukumar Isa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng