Ana Fargabar Harin Bello Turji, 'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Sokoto
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a wani kauyen jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
- Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba bayan sun farmake su da sanyoin safiya
- An rasa rayukan mutane, an jikkata wasu tare da yin awon gaba da wadanda ba a san adadinsu ba zuwa cikin daji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Akalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu, yayin da aka sace wasu uku, bayan da ’yan bindiga suka kai hari a jihar Sokoto.
'Yan bindigan sun kai harin ne a kauyen Kyara, wani kauye mai nisa da ke kan iyaka a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Bayan kashe mutane fiye da 40, Gwamna Bago ya fadi dalilin 'yan bindiga na farmakar Kasuwan Daji
'Yan bindiga sun kai hari a Sokoto
Tsagerun 'yan bindigan sun kai harin ne da sanyin safiyar ranar Alhamis, 15 ga watan Janairun 2026.
Majiyoyi sun bayyana cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:00 na safe a kauyen, wanda ke kusa da iyakar Jamhuriyar Nijar, kuma babu layin sadarwar waya a yankin.
An ce ’yan bindigan sun zo da yawa dauke da manyan makamai, inda suka mamaye kauyen suna harbi ba kakkautawa, lamarin da ya jefa mazauna cikin firgici.
An kashe mutane a harin 'yan bindiga
A yayin harin, mutane bakwai da aka harba sun mutu, yayin da wasu biyu suka jikkata da harbin bindiga.
Haka kuma an sace mutane uku, tare da kwashe dabbobi da dama, adadin da ba a bayyana ba.
Jami'an tsaro sun kai dauki
Bayan samun rahoton lamarin, jami’an tsaro na haɗin gwiwa sun garzaya yankin nan take domin kao daukin gaggawa.
Da isarsu, sun kwashe gawarwakin mamatan da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin yin binciken gawarwaki da kuma ba da kulawar gaggawa.

Source: Original
Bayan aukuwar lamarin, sojoji sun kaddamar da farautar ’yan bindigan, da nufin ceto waɗanda aka sace, dawo da dabbobin da aka sace, tare da cafke waɗanda ke da hannu a harin.
A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da sintiri a ciki da kewayen kauyen Kyara domin kwantar wa al’umma da hankula da kuma hana sake kai hare-hare.
Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga
- Tashin hankali: Ƴan bindiga sun kai mummunan hari kan ƴan sanda, an rasa rayuka
- 'Yan bindiga sun kori mutanen kauyuka a Sokoto? Gwamnati ta yi bayani
- Ruwan wuta daga sojoji ya firgita 'yan bindiga, suna rokon gwamnati sulhu
Mutane sun tsere kan barazanar Bello Turji
A wani labarin kuma, kun ji cewa barazanar hatsabibin dan bindiga, Bello Turji, ta sanya mutane na barin matsugunansu a jihar Sokoto.
Varazanar da ‘yan bindigan Bello Turji ke yi ta tilasta wa iyalai barin gidajensu, wasu kuma su rika bin hanyoyi masu hatsari domin ketare iyaka zuwa Jamhuriyar Nijar.
Majiyoyi sun bayyana cewa kauyuka 20 a sassa daban-daban na karamar hukumar Isa sun watse sakamakon tsoron hare-haren ‘yan bindiga.
Asali: Legit.ng
