Sauya Sheka: Wasu 'Yan APC na Maganar Hana Abba Takara a 2027

Sauya Sheka: Wasu 'Yan APC na Maganar Hana Abba Takara a 2027

  • Wasu mazauna jihar Kano sun yi magana kan rade-radin sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam'iyyar NNPP zuwa APC
  • Magoya bayan APC na cewa jam’iyyarsu ta riga ta tanadi tsari da dabaru, kuma duk mai shigowa sai ya bi ka’idojin da suka riga suka kafa
  • A bangaren NNPP kuwa, ana nuna fargaba cewa sauya sheka na nufin katse alaka da tafiyar Kwankwasiyya da aka riga aka kafa a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Yayin da rade-radin cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC ke kara yaduwa, tattaunawar siyasa ta fice daga majalisu da gidajen manyan ‘yan siyasa zuwa tituna da unguwanni.

Magoya bayan jam’iyyun APC da NNPP sun bayyana ra’ayoyinsu, suna nuna yadda lamarin ke jan hankali, tsoro da kuma lissafin siyasa.

Kara karanta wannan

Shiga APC: Kwankwaso ya fadi yadda Abba zai buga rikici da Ganduje

Abba Kabir Yusuf da Dan Bilki Kwamanda
Gwamna Abba Kabir Yusuf da dan APC, Dan Bilki Kwamanda. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa|Gandujiyya
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa maganganun da ake ji daga jama’a sun nuna bambancin fahimta game da abin da sauya shekar ka iya haifarwa, ko dai ga jam’iyyun biyu ko kuma ga makomar siyasar Kano.

Ra’ayin 'yan APC kan sauya shekar Abba

Wani jigo a APC, Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda, ya bayyana cewa gwamnan na nuna fargaba game da abin da zai tarar idan ya shiga APC, inda ya bukaci ya koma wajen mai gidansa, wato Rabiu Kwankwaso.

A cewarsa, APC a Kano ta fi karfin mutum guda, kuma jam’iyyar ta riga ta kammala shirye-shiryen kwato mulki a 2027. Ya ce duk wanda ya shigo APC dole ne ya fafata a zaben fidda gwani, domin babu batun tikitin kai-tsaye.

Ismail Muhammad ya ce ba duka magoya bayan NNPP ba ne za su bi gwamnan, saboda haka ya ce APC na da tsari mai karfi da zai tilasta wa duk mai shigowa ya bi tafarkin da aka riga aka shimfida.

Kara karanta wannan

Sauya shekar Abba: NNPP ta ce lokaci bai ƙure ba, tana fatan Gwamna zai hakura

Abdulmalik Hamza ya kara da cewa APC na cike da gogaggun ‘yan siyasa, kuma mutanen da gwamnan ke iya zuwa da su ba za su kai adadi ko kwarewar da ke cikin APC ba.

Abba Kabir Yusuf da Rabiu Musa Kwankwaso
Gwamna Abba Kabir tare da Rabiu Kwankwaso. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Usaini Muhammad Ibrahim ya ce shiga APC na nufin shiga gida ne da aka riga aka kafa, inda manyan shugabanni kamar Abdullahi Ganduje da Abdullahi Abbas za su yi tasiri a duk wani abu da zai biyo baya, ciki har da nade-naden mukamai.

Ra’ayin dan jam'iyyar NNPP

A bangaren NNPP, Muhammad Inuwa Auwal ya ce sauya shekar gwamna na nufin katse alaka da tafiyar Kwankwasiyya gaba daya.

Ya bayyana cewa romon dimokuradiyya koma hannun wadanda suka bi gwamnan da kuma ‘yan APC da ya shiga cikinsu, lamarin da ya ce zai shafi siyasa a Kano.

Zaman Abba da Ganduje a APC

A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi tsokaci kan zaman da Abba Kabir Yusuf zai yi da Abdullahi Ganduje.

Kwankwaso ya ce ko da Abba Kabir ya koma APC kamar yadda ake rade-radi, zai yi zaman doya da manja tsakaninsa da Ganduje.

Jagoran NNPP ya bayyana haka ne bayan Abba Kabir ya yi magana kan cewa Ganduje ya rufe cibiyoyin koyon sana'a da Kwankwaso ya kafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng