An Kori Sarki daga Fadarsa, Gwamna Zai Sanya Masa Ido bayan Dakatar da Shi

An Kori Sarki daga Fadarsa, Gwamna Zai Sanya Masa Ido bayan Dakatar da Shi

  • Gwamnatin Jihar Ekiti ta dauki mataki kan wani basarake bayan korafe-korafe da al'ummarsa ke kawo wa
  • An dakatar da Sarkin Elepe na Epe-Ekiti, Oba Williams Adesoye sakamakon zargin rashin da’a a ranar Juma'a 16 ga watan Janairun 2026
  • Matakin ya biyo bayan korafe-korafen mazauna gari da ke neman tsige shi bisa zargin danniya da mulkin kama-karya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ekiti - Gwamnatin Jihar Ekiti ta fusata game da halayyar basaraken gargajiya wanda ya tilasta dakatar da shi.

Gwamnatin ta sanya Sarkin Epe-Ekiti, Elepe, Oba Williams Adesoye, a karkashin gwaji tare da saka sunansa a jerin wadanda ake sa ido a kansu.

Gwamantin Ekiti ta dakatar da Sarki
Gwamna Biodun Oyebanjina jihar Ekiti. Hoto: Biodun Oyebanji.
Source: Twitter

Gwamnatin Ekiti ta hukunta Sarki a jihar

An dauki wannan mataki ne bayan korafe-korafe daga mazauna yankin da ke neman tsige Sarkin, suna zarginsa da rashin da'a da kuma mulkin danniya a cikin al’ummar Epe-Ekiti, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamna ya kori hadiminsa, an cafke shi yayin da ake ci gaba da bincike

Mataimakiyar Gwamnan Jihar Ekiti, Monisade Afuye, ce ta bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a fadar Ajero na Ijero-Ekiti, Oba Joseph Adewole.

Ta ce an shirya taron ne domin magance rikicin da ya dauki lokaci mai tsawo tsakanin Oba Adesoye da mutanensa, wanda ya janyo tashin hankali a yankin.

The Guardian ta ruwaito cewa rikicin ya tsananta ne bayan da aka kori babban basaraken daga fadarsa, lamarin da ya kara tayar da hankulan manya da matasan gari da ke neman a tsige shi.

Da take jawabi ga mahalarta taron, Afuye ta bukaci matasa su dakata da daukar matakai masu tsauri, tana rokon su ba Sarkin wani karin lokaci domin gyara halayyarsa.

Ta ce:

“Abin da gwamnati ke so shi ne zaman lafiya kawai. Ba za ku ci gaba da tsayawa kan matsaya mai tsauri ba. Idan akwai rikici, ci gaba ba zai samu ba.”
An taso gwamnan Ekiti a gaba ya tsige Sarki
Taswirar jihar Ekiti da ke Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Dalilin hana Sarki komawa fadarsa

A nasa bangaren, Ajero na Ijero-Ekiti, Oba Joseph Adewole, ya ce daya daga cikin shawarwarin da aka cimma shi ne hana Oba Adesoye komawa fada har sai an kammala sulhu.

Kara karanta wannan

Musulunci ya yi rashi: 'Yan bindiga sun hallaka malamin addini a Kaduna

Ya bayyana cewa za a sanya Elepe a karkashin gwaji, kuma dole ne ya rattaba hannu kan alkawarin kyautata dabi’a, yayin da hanyoyin gyara ke aiki don warware matsalolin da suka hana ci gaban gari.

Adewole ya ce:

“A lokacin wannan gwaji, gwamnati, ni kaina da al’ummar gari za mu rika sa ido a kansa. Muna fatan zai gyara halayyarsa domin jama’a su sake duba matsayinsu.”

Ya kuma gargadi matasa da kada su dauki doka a hannunsu, yana jaddada cewa akwai ka’idoji da dokoki na nadawa ko tsige sarakunan gargajiya.

Gwamna ya dawo da kwamishinoni da ya kora

Mun ba ku labarin cewa Gwamnan Biodun Iyebanji ya tura sunayen mutanen da zai nada a matsayin kwamishinoni ga Majalisar dokokin jihar Ekiti.

Gwamnatin Ekiti ta ce yawancin wadanda gwamnan ya nada suna cikin tsofaffin kwamishinonin da ya kora daga aiki a kwanakin baya.

Ta ce an dawo da kwamiahinonin ne domin gudun barakar da iya bullowa tsakanin 'ya'yan APC a zaben gwamnan da za a yi a 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.