Shekara 75 da Zuwan Inyass Katsina, Miliyoyin 'Yan Darika za Su Yi Maulidi a Jihar

Shekara 75 da Zuwan Inyass Katsina, Miliyoyin 'Yan Darika za Su Yi Maulidi a Jihar

  • Gwamna Dikko Umaru Radda, ya fara duba shirye-shirye a filin wasan Muhammadu Dikko gabanin babban taron Mauludin Tijjaniyya na kasa na shekarar 2026
  • Daga bisani gwamnan ya kai ziyara ta girmamawa ga Sarki kuma Khalifan Tijjaniyya, Muhammadu Sanusi II, domin tattauna shirye-shiryen taron
  • Ana sa ran taron zai ja hankalin sama da mutane miliyan 4 daga kasashe kusan 15, lamarin da ya kara wa taron muhimmanci ga Katsina da Najeriya baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina – Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ci gaba da daukar matakai kan shirye-shiryen karbar bakuncin Mauludin Tijjaniyya na kasa na shekarar 2026.

Ziyarar ta zo ne gabanin babban taron da ake sa ran zai gudana a filin wasan Muhammadu Dikko, wanda tuni aka fara gyare-gyare da tsare-tsare domin tabbatar da nasarar taron.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, an gano dalilai 3 da suka jawo jinkirin sauya shekar Gwamna Abba zuwa APC

Gwamna Dikko Radda da Sanusi II a shirin taron Maulidi a Katsina
Gwamna Dikko Radda ya ziyarci Sanusi II ana shirin Maulidi a Katsina. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Source: Facebook

Hadimin gwamnan, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook cewa Mauludin Tijjaniyya na kasa na daga cikin manyan tarukan addini da ke haduwa da miliyoyin mabiya darikar Tijjaniyya daga sassa daban-daban na duniya.

Gwamna Radda ya je wajen Maulidi a Katsina

Gwamna Radda ya ziyarci filin wasan Muhammadu Dikko da ke Katsina domin duba irin matakin da aka kai wajen shirin taron Mauludin na shekarar 2026.

A yayin ziyarar, gwamnan ya gana da mambobin kwamitin da ke da alhakin shirya taron, inda suka gaisa tare da tattauna batutuwan da suka shafi tsaro, masauki da saukaka zirga-zirga ga mahalarta taron.

Gwamnan ya bayyana gamsuwarsa da gyare-gyaren da ake ci gaba da yi a filin, yana mai jaddada cewa gwamnati za ta tabbatar an samar da dukkan abubuwan da suka dace domin taron ya gudana cikin kwanciyar hankali.

Ziyarar Radda ga Sarki Sanusi II

Bayan kammala duba filin taron, Gwamna Radda ya kai ziyarar girmamawa ga Mai Martaba Sarki kuma Khalifan Tijjaniyya, Muhammadu Sanusi II, a masaukinsa da ke Katsina.

Kara karanta wannan

Mutanen kauyuka za su kaura domin luguden wuta kan 'yan bindiga a dazuka

A yayin ziyarar, gwamnan da sarkin sun yi fatan alheri, tare da tattauna muhimmancin taron Mauludin Tijjaniyya ga al’umma, musamman wajen karfafa zaman lafiya da hadin kai.

Sarkin, wanda Khalifan Tijjaniyya a Najeriya da kasashen makwabta ne, ana kallonsa a matsayin daya daga cikin manyan shugabannin addini da ke da tasiri a yammacin Afirka.

Bayani kan Mauludin shekarar 2026

Taron Mauludin Tijjaniyya na kasa na shekarar 2026 na daga cikin manyan tarukan darikar Tijjaniyya da ake gudanarwa domin tunawa da Sheikh Ibrahim Nyass.

Wani rahoto ya nuna cewa ana sa ran taron zai samu halartar sama da mutane miliyan 4 daga kasashe kusan 15 a Afrika da kewaye.

Gwamna Dikko Radda a filin Maulidi a Katsina
Gwamna Dikko Radda tare da masu shirya Maulidi a Katsina. Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Taron na bana ya kuma zo da wani muhimmin tarihi, domin shi ne karo na uku da Jihar Katsina ke karbar bakuncin Mauludin na kasa, bayan wanda aka yi a shekarun 2002 da 2016.

Baya ga kasancewarsa karo na uku a Katsina, Mauludin na shekarar 2026 ya zo ne a daidai lokacin da ake cika shekaru 75 tun bayan ziyarar farko da Sheikh Ibrahim Inyass ya kai Jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kashe Naira biliyan 40 a zamanantar da gadar Legas da CCTV

Bago ya ziyarci sabon masallaci a Neja

A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamna Umaru Bago na jihar Neja ya ziyarci wani katafaren masallacin Juma'a da aka yi a birnin Minna.

Legit Hausa ta tattaro cewa gwamnan ya zagaya wurare daban-daban na sabon masallacin tare hawa kan mimbarin hudubar Juma'a.

A bayanin da ya yi bayan ganin ginin, Gwamna Bago ya yaba da gina katafaren masallacin, tare da kira a cigaba da kula da shi yadda ya kamata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng