Barazanar Bello Turji Ta Sa 'Yan Najeriya Gudun Hijira Nijar, Suna Mawuyacin Hali

Barazanar Bello Turji Ta Sa 'Yan Najeriya Gudun Hijira Nijar, Suna Mawuyacin Hali

  • Mazauna Isa a Sokoto sun bayyana yadda barazanar Bello Turji ta sa iyalai ke barin gidajensu suna tsallakawa zuwa Jamhuriyar Nijar
  • Rahotanni sun nuna cewa sama da kauyuka 20 sun watse bayan sababbin barazana da hare-haren ‘yan bindiga ya kara bulla a yankunansu
  • Wasu mazauna sun ce duk da hadarin hanya da barazanar kama su, guduwa zuwa wasu wurare kamar Nijar ya fi masu zama a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto – Wasu da suka rasa matsugunansu a karamar hukumar Isa ta Jihar Sokoto sun koka kan karuwar hare-haren ‘yan bindiga, suna cewa ‘yan uwansu na shiga hadari mai tsanani wajen tsallakawa zuwa Jamhuriyar Nijar.

Wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna jama’a na guduwa daga wasu kauyuka, lamarin da hukumomin yankin suka tabbatar da sahihancinsa.

Kara karanta wannan

"Za a iya": Jigo a ADC ya gano hanyar da 'yan adawa za su kifar da Tinubu a 2027

Dan ta'addan da ya addabi jama'a, Bello Turji
Bello Turji da ya addabi jihar Sokoto. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Sun shaida wa jaridar Punch cewa barazanar da ‘yan bindigar Bello Turji ke yi ce ta tilasta wa iyalai barin gidajensu, wasu kuma su rika bin hanyoyi masu hatsari domin ketare iyaka.

Barazanar Bello Turji ta sa mutane hijira

Sakataren Kungiyar Ci gaban Yankin Gabashin Sokoto, Farfesa Muazu Shamaki, ya bayyana cewa mutane sun fara guduwa ne bayan Bello Turji ya fitar da barazana ga al’ummomin da ke kusa da Tidibali.

A cewarsa, tun daga ranar da aka fara barazanar, mazauna yankin ke tururuwa zuwa hedkwatar karamar hukumar domin kai korafi.

Ya kara da cewa fiye da kauyuka 20 a sassa daban-daban na karamar hukumar sun watse sakamakon tsoron hare-haren ‘yan bindiga.

Turji ya sa 'yan Najeriya hijira zuwa Nijar

A bayanai daban-daban da suka fitar, wasu mazauna yankin sun ce ‘yan uwansu da iyalansu sun tsere zuwa Nijar domin neman mafaka.

Mohammed Saleh da ke yankin Dole Kena a Sabon Birni, ya ce mutane da dama sun dauki iyalansu baki daya suka nufi Nijar, wasu ma har da iyayensu.

Kara karanta wannan

Duk da harin Amurka, 'yan Sokoto sun fadi yadda barazanar Bello Turji ke tarwatsa su

Ya ce halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki a Nijar ba lallai ya kasance mai dadi ba, amma tsoron rayuwa a gida ya fi musu tsanani.

Halin da 'yan Najeriya ke ciki a Nijar

Tashar DW Hausa ta fitar da wani bidiyo kan yadda 'yan Najeriya ke zaman gudun hijira a birnin Yamai na Nijar cikin mawuyacin hali.

'Yan Najeriya sun bayyana cewa duk inda suka shiga ana korarsu, ba su samu wajen kwana ba sai suka tafi kusa da makabarta suka zauna.

Sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta kai musu dauki saboda yadda yunwa da sauran matsaloli ke addabansu.

Yadda yan Najeriya ke zaune a Nijar
'Yan Najeriya da suka fake a kusa da makabarta a Nijar. Hoto: DW Hausa
Source: Facebook

Hadarin tsallaka iyakar Najeriya da Nijar

Saleh ya ce wasu daga cikin wadanda suka tsallaka iyaka sun fuskanci matsaloli, wasu an kama su sannan aka mayar da su Najeriya.

Duk da haka, ya jaddada cewa yawancin mutane sun fi ganin guduwa ya fi aminci fiye da ci gaba da zama a karkashin barazanar ‘yan bindiga.

A cewarsa, sababbin hare-haren sun fara ne kusan makonni uku da suka wuce, inda satar mutane da neman kudin fansa ya zama ruwan dare.

Kara karanta wannan

Yaran Turji sun yi ta'asa a Sokoto bayan sakon dan ta'addan ya rikita jama'a

Bayanin dattawa da manoma a Katsina

Rahotanni sun nuna cewa Sarkin Noman Tidibali mai shekaru 75 ya ce rashin tsaro ya dade yana addabar yankin ba tare da alamar sauki ba.

Sarkin Noman ya kara da cewa bayan kama mutane, sau da dama ana biyan kudin fansa amma ba a saki wadanda aka sace ba, lamarin da ya kara tsoratar da jama’a.

Wani dattijo mai shekaru 66, Malam Ibrahim, ya ce ya tsere da iyalansa bayan samun labarin barazanar da ke da alaka da Bello Turji, yana mai cewa za su jira karin bayani kafin yanke shawarar komawa gida.

An harbe matar Sarkin Noma a Neja

A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun harbe matar wani Sarkin Noma a jihar Neja.

An ce 'yan ta'addan sun kashe matar ne a lokacin da suka kai wani kazamanin hari a wasu kauyuka da ke karamar hukumar Borgu.

Yayin da suka shiga kauyukan, sun bude wuta kan jama'a, lamarin da ya firgita kowa da kowa, mutane suka fara gudun neman tsira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng