Wace Cuta ke Damunsa? An Kwantar da Sarkin Saudiyya a Asibiti, Sanarwa Ta Fito

Wace Cuta ke Damunsa? An Kwantar da Sarkin Saudiyya a Asibiti, Sanarwa Ta Fito

  • Masarautar Saudiyya ta tabbatar da cewa an kwantar da Sarki Salman Bin Abdul'aziz a wani asibiti a Riyadh, babban birnin kasar
  • A wata sanarwa da hukumomin Saudiyya suka fitar, an ce za a yi wa Sarki Salman wasu gwaje-gwaje a asibin King Faisal Specialist
  • Duk da ba a cika magana kan rashin lafiyar Sarkin Saudiyya ba, amma ya sha kwanciya a asibiti ana masa gwaje-gwaje a shekarun baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Riyadh, Saudi Arabia - Rahotanni daga kasar Saudiyya na nuna cewa Sarki Salman bin Abdul'aziz na kwance a asibiti za a yi masa wasu gwaje-gwaje a birnin Riyadh.

Masarautar Saudiyya ta sanar a ranar Juma’a, 16 ga watan Janairu, 2026 cewa za a yi wa Sarki Salman bin Abdulaziz, mai shekaru 90, wasu gwaje-gwajen lafiya a wani asibiti da ke babban birnin ƙasar, Riyadh.

Kara karanta wannan

2027: Jihohin Arewa 19 za su tsaida wanda za su zaba tsakanin Tinubu da Atiku

Sarki Salman.
Sarkin kasar Saudiyya, Salman Bin Abdul'aziz Hoto: Inside The Haramain
Source: Twitter

Hukumar da ke kula da manyan masallatai biyu masu alfarma na kasar Saudiyya ta wallafa sanarwar da masarautar ta fitar a shafinta, Inside The Haramain, na manhajar X.

Me za a yi wa Sarki Salman a asibiti?

A cikin sanarwa wacce ta fito daga Masarautar Saudiyya kuma kafafen yaɗa labaran gwamnatin kasar suka wallafa, an ce:

“Babban mai kula da Masallatan Harami guda biyu, Allah Ya kara kare shi, na kwance za a yi masa wasu gwaje-gwajen lafiya a yau a asibitin King Faisal Specialist da ke birnin Riyadh.”

Saudiyya, wadda ita ce ƙasa lamba daya da ke fitar da ɗanyen mai a duniya, ta shafe shekaru tana ƙoƙarin kawar da jita-jitar da ake yi kan lafiyar Sarki Salman.

Sarki Salman ya hau karagar mulki ne a shekarar 2015, sai dai a 2017 aka naɗa ɗansa Mohammed bin Salman a matsayin yarima mai jiran gado, wanda shi ne ke gudanar da harkokin mulki a zahiri.

Kara karanta wannan

Rai bakon duniya: Malamin Musulunci da ya ceci Kiristoci 260 a rikicin Plateau ya rasu

Tarihin yanayin lafiyar Sarkin Saudiyya

Ba a yawan tattauna batun lafiyar Sarki Salman bin Abdulaziz a bainar jama’a, sai dai a cikin ‘yan shekarun nan an kwantar da shi asibiti sau da dama domin tiyata da gwaje-gwaje.

A shekarar 2024, gwamnatin Saudiyya ta bayyana cewa Sarkin ya kamu da cututtukan huhu, amma daga baya ya warke.

A watan Mayu 2022, an kwantar da shi asibiti domin a yi masa duban hanji, inda ya shafe sama da mako guda ana yi masa wasu gwaje-gwaje da kuma hutawa.

Sarki Salman.
Sarki Salman bin Abdul'aziz na kasar Saudiyya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Haka kuma, a Maris 2022, an sake kwantar da shi asibiti domin yin wasu gwaje-gwajen lafiya, tare da canza baturin na’urar bugun zuciya da ke jikinsa.

Tun a shekarar 2020, aka yi qa Sarki Salman tiyata domin cire marar ƙwai. Masarautar ba ta bayyana ko gwaje-gwajen na yanzu suna da alaƙa da wata cuta ta musamman ba.

Saudiyya ga gargadi Najeriya kan marayu

A wani rahoton, kun ji cewa Saudiyya ta bayyana cewa watsi da marayu da yara marasa galihu na daga cikin abubuwan da ke rura wutar matsalar tsaro a Najeriya.

Kara karanta wannan

Zafin siyasa bai hana aiki: Abba ya fadi shirin gwamnati a kan matasa 50, 000 a Kano

Saudiyya ta garhadi Najeriya da ta kula marayu da yara masu gararamba a gari domin hana au fada wa miyagun ayyuka da ka iya zama barazana ga tsaro.

Wannan gargadi ya fito ne daga wakilan kasar ta Saudiyya yayin wani shirin tallafawa marayu sama da 1,000 a jihar Kwara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262