Anas Aremeyaw: An Kaddamar da Shirin Horar da Ƴan Jaridar Arewa kan Amfani da Fasahar AI
- Kamfanin WikkiTimes ya ƙaddamar da shirin "Anas Aremeyaw Anas AI Accountability Fellowship" ga ƴan jarida a Arewacin Najeriya
- Wannan shiri na tsawon watanni shida zai horar da manema labarai yadda za su yi amfani da fasahar AI domin gudanar da ayyukan bincike
- Wadanda suka yi nasarar shiga shirin za su karɓi horo daga manyan masana, alawus duk wata, da tallafi domin samar da rahotanni na bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi — WikkiTimes ta ƙaddamar da Anas Aremeyaw Anas AI Accountability Fellowship, wani shiri na aikin jarida da aka tsara don inganta rahotannin bincike kan masana'antun hakar ma'adinai da matsalolin muhalli a Arewacin Najeriya.
An sanar da shirin ne ta hanyar gidauniyar "WikkiTimes Media Foundation" kuma zai mayar da hankali ne ga ƴan jarida da ke aiki a garuruwan da ayyukan hakar ma'adinai da suke lalatawa muhalli.

Source: UGC
Mayar da hankali kan rahotannin hakar ma'adinai
A shafinta na yanar gizo, jaridar WikkiTimes ta bayyana cewa an ƙirƙiri shirin ne sakamakon yadda ayyukan hakar ma'adinai ke ƙaruwa a jihohi da dama na Arewa, gami da ƙarancin rahotannin kafafen yaɗa labarai kan cin zarafin da ke da alaƙa da fannin.
A cewar kamfanin, garuruwan yankin na fuskantar ƙalubale kamar hakar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, lalacewar muhalli, satar albarkatu, raba mutane da muhallansu, da kuma rashin tsauraran matakan sa ido.
Sannan kamfanin ya ce duk da wadannan tarin kalubale, galibi kafofin watsa labarai na cikin gida ba sa da kayan aiki da ƙwarewar bincikar waɗannan matsalolin.
Ana sa ran shirin zai tallafa wa ƴan jarida masu ba da rahotannin waɗannan garuruwan ta hanyar ba su horo da tallafin gudanar da aiki.
Dalilin sanya wa shirin sunan Anas
An sanya wa shirin sunan kwararren ɗan jaridar binciken kwakwaf din nan na ƙasar Ghana, Anas Aremeyaw Anas, wanda aka sani da gudanar da bincike na sirri da tattara kwararan shaidu.

Kara karanta wannan
Duk da harin Amurka, 'yan Sokoto sun fadi yadda barazanar Bello Turji ke tarwatsa su
Yayin da yake jawabi kan shirin, Haruna Mohammed Salisu, mawallafin WikkiTimes, ya ce shawarar sanya sunan Anas ta ginu ne bisa jajircewarsa ga aikin jarida na tabbatar da gaskiya.
Jaruna Salisu ya tuna ziyarar da Anas ya kai Gombe a shekarar 2024 don halartar wani taro da WikkiTimes da Jami'ar Northeastern suka shirya.
Mawallafin jaridar ya ce Anas ya yi tafiyar dare a mota bayan ya rasa jirgin sama daga Abuja domin kawai ya halarci taron.
"Ya yi yekuwar cewa matasan ƴan jaridar da muka tara sun cancanci ƙarfafawa," in ji Salisu, inda ya ƙara da cewa ziyarar ta ƙarfafa gwiwar ɗalibai da sababbin ƴan jarida da suka halarci taron.
Tsarin shirin Anas Aremeyaw Anas
WikkiTimes ta ce shirin zai gudana ne na tsawon watanni shida kuma za a raba shi gida biyu, in ji rahoton My Joy Online.
Mataki na farko zai ɗauki watanni uku kuma zai mayar da hankali ne kan horarwa. Mahalarta za su sami horo kan aikin jarida da taimakon AI, binciken bayanan sirri daga tushe (OSI), nazarin hotunan tauraron ɗan adam, tantance bayanan zamani, tsaro, da bayar da rahotannin hakar ma'adinai.
Mataki na biyu kuma zai kasance na aikace-aikace na tsawon watanni uku. A wannan lokacin, mahalarta za su yi aiki tare da editoci a WikkiTimes don samar da rahotannin bincike kan harkokin gudanarwa a fannin hakar ma'adinai da matsalolin muhalli.

Source: Twitter
Tallafi ga wadanda za su shiga shirin
Rahoton jaridar ya nuna cewa wadanda aka zaba don samun hoton za su samu jagoranci daga editoci, alawus na kowane wata, da kuma damar yin amfani da kayan aikin bincike na zamani.
Ana sa ran kowane mutum daga cikin masu cin gajiyar shirin zai kammala aƙalla bincike guda ɗaya tare da haɗin gwiwar WikkiTimes.
A ƙarshen shirin, mahalarta za su karɓi takardar shaidar kammalawa wadda Anas Aremeyaw Anas zai sanya wa hannu da kansa.
Kasashe 10 da 'yan jarida ba su da 'yanci
A wani labari, mun ruwaito cewa, akwai wasu ƙasashe 10 na duniya waɗanda ƴan jarida ba su da cikakken ƴancin gudanar da ayyukansu kamar yadda doka ta ba su dama.
Ƴancin ƴan jarida yana ba su damar yin bincike tare da kawo rahoto kan abubuwan da suka shafi jama'a ba tare da tsoron fuskantar takura ko barazana ba.
Sai dai, kasashen duniya kamar Eritrea, Syria, Afghanistan da wasu bakwai sun kasance suna tauye wannan 'yanci, lamarin da ke jefa 'yan jarida a tsangwamar gwamnati.
Asali: Legit.ng

