Rokici Ya Dauki Zafi, Babbar Kotu Ta Tsoma Baki kan Yunkurin Tsige Gwamna Fubara
- Babbar kotun jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Nma Odu
- Kotun ta dauki wannan mataki ne bayan amincewa da bukatar gaggawa da Gwamna Fubara da Farfesa Odu suka shigar gabanta
- Ta umarci babban alkalin Rivers, Mai shari’a Simeon Chibuzor Amadi da kar ya bi umarnin da Majalisa ta aiko masa kan shirin tsige gwamna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Babbar Kotun Jihar Rivers da ke zamanta a birinin Fatakwal ta tsoma baki kan dambarwar siyasa da ke faruwa tsakanin Majalisar dokoki da Gwamna Siminalayi Fubara.
Kotun ta hana babban alkali, Mai shari’a Simeon Chibuzor Amadi, karɓa ko yin aiki da kowace wasika daga Majalisa da ta shafi yunkurin tsige Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Nma Odu.

Source: Twitter
Gwamna Fubara ya kai kara kotu

Kara karanta wannan
Rikici ya dawo 'danye, 'Yan Majalisa 4 sun canza tunani kan yunkurin tsige Gwamna Fubara
Vangaurd ta tattaro cewa kotun da ke yankin ƙaramar hukumar Oyibo, a Fatakwal, ta bayar da umarnin ne bayan shigar da ƙorafe-ƙorafe biyu gabanta.
Gwamna Fubara da Farfesa Odu ne auka shigar da kararrakin guda biyu a gaban kotu, masu lambobin OYHC/7/CS/2026 da OYHC/6/CS/2026.
Kotun ta hana Kakakin Majalisar Dokokin Rivers, Rt. Hon Martin Amaewhule, tare da wasu mutane 32 da suka haɗa da Babban Alkalin Jiha, ɗaukar duk wani mataki da ya shafi shirin tsige gwamnan da mataimakiyarsa.
Hakan na kunshe ne a cikin umarnin wucin gadi da kotun ta bayar a zamanta na yau Juma'a, 16 ga watan Janairu, 2026.
Umarnin da kotu ta ba babban alkalin Rivers
Bugu da kari, kotun ta hana Mai shari’a Amadi karɓa, turawa, nazari ko aiki da duk wata buƙata, kuduri, takardar tsige gwamna ko kowace irin sadarwa daga waɗanda ake ƙara na 1 zuwa na 27.
Kotun ta hana babban alkalin kafa kwamitin bincike kan zargin rashin da’a da ake yi wa gwamna da mataimakiyarsa, na tsawon kwanaki bakwai.
Mai shari’a F. A. Fiberesima, wanda ya jagoranci zaman kotun, ne ya yanke wannan hukunci yayin da ya amince da buƙatun gaggawa da Gwamna Fubara da mataimakiyarsa suka shigar.

Source: Getty Images
Yadda za a isar da umarnin kotu
Kotun ta kuma ba wa masu ƙarar izinin isar da umarnin wucin-gadin da takardun shari’ar ta hanyar liƙa su a ƙofar zauren Majalisar Dokokin Jihar Rivers.
Haka kuma, kotun ta umurci a isar da takardar wannan umarni ga wanda ake ƙara na 32, wato Babban Alkalin Jihar Rivers, ta hannun ma’aikacin shari’a da ke aiki a ofishinsa.
Daga bisani, kotun ta ɗage ƙarar zuwa 23 ga Janairu, 2026, domin sauraron cikakkiyar karar da aka kai gabanta, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Mambobi 4 sun canza tunani kan Fubara
A wani labarin, kun ji cewa 'yan Majalisar Dokokin Jihar Rivers hudu sun canza tunani kan matsayarsu ta janyewa daga shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara.
Yan majalisar sun sauya shawararsu, inda suka bayyana cikakken goyon bayansu ga shirin tsige gwamnan da mataimakiyarsa.
Wannan mataki na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan 'yan Majalisar hudu sun yi kiran a sasanta rikicin siyasar da ya girgiza jihar cikin ruwan sanyi.
Asali: Legit.ng
