Sojoji Sun Saki Bam kan 'Yan Ta'addan ISWAP bayan Taruwa a karkashin Bishiya
- Sojojin rundunar Operation HADIN KAI sun dakile wani mummunan hari da ‘yan ISWAP suka kai a sansanin soji a Azir da ke Damboa
- Biyo bayan lamarin, rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kai farmakin da ya tarwatsa ‘yan ta’addan tare da hallaka da dama daga cikinsu
- Makaman yaki da alburusai masu yawa ne aka kwato bayan ‘yan ISWAP sun tsere daga filin daga da suka ji wuta daga hannun sojoji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno – Sojojin Najeriya dake karkashin rundunar Operation HADIN KAI sun dakile wani hari da ‘yan kungiyar ISWAP suka kai kan sansanin soji a yankin Azir, karamar hukumar Damboa a Jihar Borno.
Harin, wanda ya auku da sassafe, ya gamu da martani mai karfi daga sojojin kasa tare da tallafin jiragen yaki na Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, lamarin da ya tilasta ‘yan ta’addan tserewa bayan sun sha wuta.

Source: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa hadin gwiwar sojojin kasa da na sama ne ya kai ga tarwatsa shirin ISWAP na mamaye sansanin tare da hallaka su.
Sojoji sun dakile harin ISWAP
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan ISWAP sun yi yunkurin karya katangar tsaron sansanin sojin Azir da ke Damboa. Sai dai sojojin dake bakin aiki sun yi gaggawar mayar da martani.
An bayyana cewa sojojin sun nuna jarumtaka matuka, inda suka fuskanci maharan na tsawon fiye da awa guda suna fafatawa ba tare da ja da baya ba.
Tallafin jiragen yaki na rundunar Operation Hadin Kai ya kara karfin farmakin, lamarin da ya durkusar da ‘yan ta’addan baki daya.
An saki bama-bamai kan ISWAP
Bayan dakile harin a sansanin, jami'an leken asiri da sa ido sun bi sawun ‘yan ta’addan da suka tsere. Wannan ya bai wa rundunar sojin sama damar kai farmaki kan hanyoyin da maharan suka bi wajen guduwa.
Majiyoyi sun ce da misalin karfe 1:40 na dare aka tura jiragen yaki domin ba da taimako kai tsaye. A lokacin da suka isa sama da Azir, matukan jiragen sun hango sojojin kasa na harbi zuwa inda ‘yan ta’addan ke tserewa.
Sakon da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a X ya ce an gano ‘yan ISWAP suna taruwa karkashin bishiyoyi suna neman mafaka, lamarin da ya sa jiragen suka kai farmaki kansu.

Source: Facebook
Majiyoyin sun tabbatar da cewa farmakin ya cimma nasara, inda aka hallaka ‘yan ta’adda da dama tare da rage karfinsu na sake haduwa ko kai wani hari a yankin.
'Yan bindiga sun harbe matar Sarki
A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kai mummunan hari karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shiga garin da suka farmaka ne da dare, inda suka lalata dukiya mai yawa da raunata mutane.
Matar sarkin noman Kebe mai shekara 75 ta fake a wani waje amma 'yan ta'addan suka ganta a lokacin da suke wucewa kuma nan take suka harbe ta.
Asali: Legit.ng

