Ruwan Wuta daga Sojoji Ya Firgita ’Yan Bindiga, Suna Rokon Gwamnati Sulhu

Ruwan Wuta daga Sojoji Ya Firgita ’Yan Bindiga, Suna Rokon Gwamnati Sulhu

  • Gwamnatin Kogi ta ce matsin lamba da ruwan wuta daga jami’an tsaro ya tilasta wa wasu ’yan bindiga neman sulhu da mika makamansu
  • Mai bai wa gwamna shawara kan tsaro ya ce amfani da fasaha da kayan aiki ya raunana ’yan ta’adda sosai
  • Gwamnati ta jaddada matsayarta game da tattaunawa da ’yan bindiga ba, tana shirin kafa doka da za ta haramta zama a daji a fadin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lokoja, Kogi - Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana cewa jami'an tsaro na ci gaba da ruwan bama-bamai kan yan ta'adda.

Gwamnatin jihar ta ce tsauraran matakan tsaro da ruwan wuta sun sa wasu ’yan bindiga fara neman sulhu da rungumar zaman lafiya.

Gwamnatin Kogi ta bayyana yadda ake nakasa yan bindiga
Gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi. Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo.
Source: Facebook

Ta'addanci: Gwamnatin Kogi na samun galaba

Mai bai wa gwamna shawara kan tsaro, Jerry Omodara ya bayyana hakan ga manema labarai a Lokoja ranar Juma’a 16 ga watan Janairun 2026, cewar Aminiya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun mamayi mutane, sun tafka barna a babbar kasuwa a jihar Zamfara

Ya ce hare-haren da aka kai wa maboyar ’yan bindiga da rusa wuraren aikata laifukansu ne suka sa suke kokarin ajiye makamai.

Omodara ya ce gwamnatin Gwamna Usman Ododo ta yi amfani da fasaha tsawon shekaru biyu wajen dakile rashin tsaro a sassan jihar.

A cewarsa, amfani da bayanan sirri da dabarun zamani ya taimaka wajen fin karfin ’yan ta’adda da ke addabar al’ummar Kogi.

Ya tunatar da cewa a ranar rantsuwarsa, Gwamna Ododo ya dauki alkawarin kare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar.

Matsayar gwamnatin Kogi kan sulhu da yan bindiga

Omodara ya ce an samar da motocin Hilux, Sienna da babura ga sojoji, ’yan sanda, JTF da ’yan sa-kai domin kara karfin aiki.

Ya bayyana cewa manufar gwamnati ita ce ci gaba da kai farmaki ga ’yan ta’adda ba tare da shiga tattaunawa da su ba.

A cewarsa, ana shirin kafa doka da za ta hana zama a daji, inda duk mazauna Kogi za su zauna ne a gari.

'Yan bindiga na shan ruwan wuta a Kogi
Taswirar jihar Kogi da yan bindiga suka addaba. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda aka gano masu taimakon ta'addanci

Omodara ya kara da cewa an gano wasu ’yan cikin gida da ke taimaka wa ’yan bindigar da ke kaura daga Arewa ta Yamma.

Kara karanta wannan

'Dabarar da sojoji ke yi wurin kubutar da mutane daga ƴan bindiga': Ministan tsaro

Ya ce gwamnati da jami’an tsaro na ci gaba da kai wa dukkan ’yan bindiga da masu taimaka musu farmaki ba sassauci.

Duk da kalubalen tsaro, Omodara ya jaddada cewa Kogi ita ce jiha mafi aminci a Arewa ta Tsakiya, cewar Tribune.

Ya danganta nasarar tsaron jihar da hadin kai, tattara bayanan sirri, da goyon bayan Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Ododo.

Jami'an tsaro sun fatattaki yan bindiga

Mun ba ku labarin cewa ‘yan sanda a jihar Kogi sun bayyana nasarar da suka samu inda suka lallasa ‘yan bindiga da dama a jihar.

Rahoto ya bayyana yadda jami’an tsaro suka lalata kayan aikin ‘yan ta’adda, tare da fatattakarsu a wani yankin jihar Kogi.

Jihar Kogi na daga cikin jihohin Arewa da ke fama da barnar ‘yan bindiga a ‘yan shekarun bayan nan, musamman 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.