Bayan Sule Lamido, Kotun Koli Ta Yi Hukunci kan Zargin 'Dansa da Cin Hanci

Bayan Sule Lamido, Kotun Koli Ta Yi Hukunci kan Zargin 'Dansa da Cin Hanci

  • Kotun Koli ta ƙi amincewa da ƙarar Aminu Sule Lamido, ɗan tsohon gwamnan Jigawa, kan hukuncin rashin bayyana $40,000
  • EFCC ta cafke Aminu a 2012 a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda ya bayyana $10,000 kawai amma aka gano ƙarin $40,000
  • Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin kotunan ƙasa da na ɗaukaka ƙara, tare da umarnin kwace kashi 25 na kuɗin da bai bayyana ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kotun Koli ta Najeriya ta raba gardama game da shari'ar dan tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido.

Kotun ta yi watsi da ƙarar da Aminu Sule Lamido, ɗan tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya shigar domin ƙalubalantar hukuncin da aka yanke masa.

Kotu ta tabbatar da c gaba da shari'ar dan Sule Lamido
Dan tsohon gwamnan Jigawa, Aminu Sule Lamido. Hoto: Aminu Sule Lamido.
Source: Twitter

Tuhumar da ake yi wa Aminu Sule Lamido

Kara karanta wannan

Shari'ar badakalar N1.35bn: Sule Lamido da 'ya'yansa sun san makomarsu

Ƙarar ta shafi hukuncin da kotun farko ta yanke, wadda ta same shi da laifin rashin bayyana kuɗaɗen waje har dala $40,000 a filin jirgin sama, cewar TheCable.

Jami’an Hukumar EFCC sun cafke Aminu ne a ranar 11 ga Disamba, 2012, a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, yayin da yake shirin hawa jirgi zuwa birnin Alkahira na ƙasar Masar.

Masu gabatar da ƙara sun bayyana cewa Aminu ya sanar da Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) cewa yana da dala $10,000 kacal, amma daga baya aka gano yana ɗauke da ƙarin dala $40,000 da bai rubuta a takardar bayyana kuɗi ba.

An yanke hukunci kan zargin badakala daga dan Sule Lamido
Harabar Kotun Koli da ke birnin Abuja. Hoto: Supreme Court of Nigeria.
Source: Twitter

Zargin da EFCC ke yiwa Aminu Sule Lamido

Hukumar EFCC ta gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kano bisa tuhuma guda ɗaya ta ƙarya wajen bayyana kuɗaɗen waje, wanda ya saɓa da dokar Hana Safarar Kuɗi ba bisa ƙa’ida ba (Money Laundering Act).

A ranar 12 ga Yulin 2015, Babbar Kotun Tarayya ta same shi da laifi, tare da umarnin ya mika kashi 25 cikin 100 na kuɗin da bai bayyana ba ga gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

EFCC ta bude wa tsohon gwamna Yahaya Bello aiki, ta kawo hujjoji a kansa a kotu

Bayan rashin gamsuwa da hukuncin, Aminu ya garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Kaduna, inda ya nemi a soke hukuncin da umarnin kwace kuɗin.

Sai dai a hukuncin da aka yanke a ranar 7 ga Disamba, 2015, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi watsi da ƙarar, tare da tabbatar da hukuncin kotun farko.

Har ila yau, Aminu bai gamsu ba, ya sake kai ƙara Kotun Koli, yana neman a soke dukkan hukuncin da aka yanke masa a kotunan ƙasa, cewar Punch.

A ƙarshe, a hukunci ɗaya tilo da alkalai suka yanke, Kotun Koli ta ƙi amincewa da ƙarar, tare da tabbatar da hukuncin da kotunan ƙasa da na ɗaukaka ƙara suka yanke a kansa.

Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar Sule Lamido

Mun ba ku labarin cewa Kotun Koli ta soke hukuncin Kotun Daukaka Kara da ta wanke tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido.

Hakan ya biyo bayan zarginsa da ’ya’yansa daga zargin safarar kudi wanda ya kai har Naira miliyan N1.35bn wanda ta kai shekaru 10.

Hukuncin ya zo ne bayan hukumar EFCC ta kalubalanci matakin Kotun Daukaka Kara da ta ce kotun farko ba ta da hurumin sauraron shari’ar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.