A Karon Farko, El Rufai Ya Yabi Gwamnati bayan Zazzafar Adawa da Kamun Ludayin Tinubu

A Karon Farko, El Rufai Ya Yabi Gwamnati bayan Zazzafar Adawa da Kamun Ludayin Tinubu

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yaba wa gwamnatin tarayya bisa tsayuwarta na kin biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane
  • El-Rufai ya shawarci gwamnatin Bola Tinubu da ta faɗaɗa wannan saƙo domin ya isa ga jama’a da dama, domin sakon ya isa ga kowa da kowa
  • Kalamansa na zuwa bayan Ministan tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya jaddada cewa ana kuɓutar da waɗanda aka sace ba tare da biyan fansa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna –Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya yabi gwamnatin tarayya a karon farko a cikin lokaci mai tsawo.

El-Rufa'i ya yi yabon ne bisa matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka kan yaƙi da garkuwa da mutane, bayan Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya ya jadda matsayarta.

Kara karanta wannan

ADC: Momodu ya kare Atiku kan zargin shirin amfani da kuɗi wajen sayen takara

Nasir El-Rufa'i ya yabi gwamnatin Tinubu
Tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i, Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: @elrufai, @DOlusegun
Source: Twitter

A hira da Janar Christopher Musa ya yi da BBC Hausa ya sake jaddada cewa gwamnatin Najeriya ba ta biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane.

Nasir El-Rufa'i ya yabi gwamnatin Bola Tinubu

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Nasir El-Rufai, wanda a lokacin mulkinsa ya sha nuna adawa da biyan fansa, ya ce wannan matsayi na gwamnati ya yi dai-dai.

El-Rufa'i ya kara da cewa ya kamata a karfafa wa gwamnati gwiwa a kan wannan mataki, domin hakan zai taimaka wa Najeriya wajen yaki da tsaro.

A hirar da ya yi, Janar Musa ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana tsayawa kan manufarta, duk da raɗe-raɗin da ake yaɗawa a tsakanin jama’a, musamman a lokutan da aka sace ɗalibai ko matafiya.

El-Rufa'i ya yi wa Janar Christopher Musa mai ritaya da tsaron kasar nan fatan nasara
Janar Christopher Musa mai ritaya a lokacin yana rundunar sojin Najeriya da tawagarsa Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Ya ce dabarar gwamnati ita ce matsin lambar sojoji da amfani da bayanan sirri domin ceto waɗanda aka sace ba wai biyan kudin fansa ba.

Kara karanta wannan

'Dabarar da sojoji ke yi wurin kubutar da mutane daga ƴan bindiga': Ministan tsaro

Ministan ya ce:

“Gwamnatin tarayya ba ta biyan kuɗin fansa. Ko da wasu suna biya, gwamnatin tarayya ba ta biya. Ba ma biyan kuɗin fansa.”

Wannan kalamai sun sake jaddada matsayin gwamnati na cewa tattaunawa da ’yan bindiga na ƙara ƙarfafa laifuka ne, ba rage su ba.

Shawarar El-Rufai ga gwamnatin Najeriya

Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya bayyana kalaman Ministan tsaro a matsayin abin da zai kwantar da hankalin ’yan Najeriya.

Ya rubuta cewa:

“Allah ya saka wa Minista Chris Musa da alheri, Allah SWT ya taimake shi a ƙoƙarinsa na gaskiya wajen samar da ingantaccen tsaro.”

Har ila yau, El-Rufai ya ba da shawarar a sake yada hirar a cikin harshen Turanci domin ta isa ga jama’a da dama.

Ana son El-Rufa'i ya dawo da Tinubu APC

A baya, mun wallafa cewa wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Kebbi, Malam Salihu Isa Nataro, ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ɗauki matakin gaggawa domin dawo da Nasir El-Rufa'i APC.

Kara karanta wannan

"Abokin barawo": Ministan tsaro ya gargadi Sheikh Gumi da masu goyon bayan 'yan ta'adda

Nataro, wanda ya taɓa tsayawa takarar gwamna a Kebbi a ƙarƙashin APC, ya ce halin da siyasar Arewa maso Yamma ke ciki a halin yanzu na buƙatar matakai masu ƙarfi domin ƙarfafa wa Shugaba Tinubu.

Ya bayyana cewa bayan sauke Dr Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin APC na ƙasa, yankin Arewa maso Yamma ya rasa wani babban ginshiƙi da ke iya haɗa jama’a tare da jawo cikakken goyon baya ga Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng