Shari'ar Badakalar N1.35bn: Sule Lamido da 'Ya'yansa Sun San Makomarsu

Shari'ar Badakalar N1.35bn: Sule Lamido da 'Ya'yansa Sun San Makomarsu

  • Kotun Koli ta soke hukuncin Kotun Daukaka Kara da ta wanke tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, da ’ya’yansa daga zargin safarar kudi
  • Kotun ta ce Sule Lamido da sauran wadanda ake kara na da amsar da za su bayar, sai ya mayar da shari’ar zuwa Kotun Tarayya don ci gaba da saurare
  • Hukuncin ya zo ne bayan hukumar EFCC ta kalubalanci matakin Kotun Daukaka Kara da ta ce kotun farko ba ta da hurumin sauraron shari’ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kotun Koli ta soke hukuncin Kotun Daukaka Kara da ya sallami tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, da ’ya’yansa biyu, Mustapha da Aminu Lamido, daga zargin safarar kudi.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ranar Juma’a, 16 ga watan Janairu, 2026 bayan kararraki daban-daban da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shigar.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci a karar da gwamnatin tarayya ta shigar da Sanata Natasha

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar Sule Lamido da yaransa
Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido da ɗansa, Mustapha Lamido. Hoto: Sule Lamido
Source: Facebook

Jaridar Premium Ties ta wallafa cewa kwamitin alkalai biyar na Kotun Koli ne ya yanke hukuncin, kuma baki dayansu sun yi tarayya wajen soke hukuncin karamar kotu.

Kotu koli ta soke hukuncin baya

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa alkalin da ya karanta hukuncin, Mai Shari’a Abubakar Umar, ya bayyana cewa kotun ta soke hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke a ranar 25 ga Yuli, 2023, a Abuja.

Hakazalika, kotun ta tabbatar da hukuncin da Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu na Kotun Tarayya, Abuja, ta yanke tun da farko, wanda ya ce akwai shari'a a tsakanin Sule Lamido da sauran wadanda ake kara da EFCC.

Kotun Koli ta kuma bayar da umarnin a mayar da shari’ar zuwa Kotun Tarayya ta Tarayya, Abuja, domin a ci gaba da sauraron ta daga inda aka tsaya.

Yadda EFCC ta fara shari'a da Sule Lamido

A shekarar 2015 ne EFCC ta gurfanar da Sule Lamido, ’ya’yansa biyu da wasu kamfanoninsu a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja, kan tuhume-tuhume 37 na safarar kudi.

Kara karanta wannan

Badakalar N1.35bn: Sule Lamido, ɗansa za su san makomarsu, Kotun Koli za ta yi hukunci

Tin a wancan lokaci, EFCC na zargin an yi safarar kudi da yawansu ya kai kimanin Naira biliyan 1.35. Hukumar ta zargi Sule Lamido da aikata wadannan laifuffuka ne a lokacin da yake gwamnan Jihar Jigawa.

EFCC ta ce Sule Lamido ya yi amfani da mukaminsa tsakanin shekarun 2007 zuwa 2015 wajen koye kudin da ake zargin ya karba a matsayin rashawa daga kwangilolin gwamnatin jihar.

Sauran wadanda ake kara a shari’ar sun hada da ’ya’yansa Aminu da Mustapha Lamido, Aminu Wada Abubakar, da kuma kamfanoninsu Bamaina Holdings Limited da Speeds International Limited.

Dalilin Sule Lamido na kai PDP kotu

A baya, mun kawo labain cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi magana kan karar da ya shigar da jam'iyyar PDP gaban kotu, inda ya ce ya yi haka ne saboda kankaro mutuncinsa.

Sule Lamido ya bayyana cewa ya kai karar ne domin kawo karshen tauye masa hakkinsa na tsayawa takarar shugaban jam’iyyar PDP na kas kamar yadda dokar kasa da jam'iyya ta ba shi dama.

Tsohon gwamnan ya nuna takaicinsa kan halin da PDP ta tsinci kanta, yana mai cewa kauna, haɗin kai da amana da suka kasance a jam’iyyar sun dusashe, lamarin da ya jawo barakar da ake samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng