Rai Bakon Duniya: Malamin Musulunci da Ya Ceci Kiristoci a Rikicin Plateau Ya Rasu
- Limamin kauyen Nghar a Plateau, Abubakar Abdullahi, wanda ya kare Kiristoci 262 a rikicin 2018, ya rasu yana da shekaru 90
- Iyalan limamin sun ce ya rasu ne a Jos bayan fama da ciwon zuciya, kwanaki 10 bayan kwantar da shi asibiti
- Marigayin ya shahara bayan ya ɓoye Kiristoci a masallaci da gidansa, har ya samu lambar yabo ta Amurka a 2019
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - An shiga jimami a jihar Plateau bayan sanar da rasuwar babban limamin Musulunci yana da shekaru 90.
Limamin kauyen Nghar da ke Karamar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Plateau, Malam Abubakar Abdullahi, ya rasu bayan fama da rashin lafiya.

Source: Instagram
An yi rashin malamin Musulunci a Plateau
Ɗansa, Saleh Abubakar, ya tabbatar wa Daily Trust rasuwar mahaifinsa a ranar Juma’a, yana mai cewa ya rasu ne a daren Alhamis 15 ga watan Janairun 2026.
Ya ce mahaifinsa ya rasu a Asibitin Kwararru na Plateau da ke Jos, kwanaki 10 bayan an kwantar da shi domin jinya.
A cewarsa, likitoci sun fara gano yana fama da matsalar zuciya, kuma tun daga lokacin lafiyarsa ba ta da tabbas.
Ya ce:
“Ya rasu kwanaki 10 bayan kwantar da shi asibiti, da farko an gano yana fama da matsalar zuciya, ya kan je dubiya, sannan ya dawo gida, lafiyarsa ba ta daidaitu ba tun bayan gano cutar zuciyar.”
Marigayin ya rasu yana da shekaru 90, inda ya bar ‘ya’ya 19, ciki har da maza 12 da mata bakwai.

Source: Original
Yadda malamin ya samu daukaka a duniya
Limamin ya yi suna ne a watan Yunin 2018, lokacin da rikicin addini ya barke a kauyuka 10 na Barkin Ladi inda ya killace Kiristoci fiye da 200 a cikin masallaci.
A wancan lokaci, ya ɓoye Kiristoci 262 a cikin masallaci da kuma gidansa, har rikicin ya lafa, lamarin da ya ceci rayukansu, cewar TheCable.
Saboda wannan jarumtaka, Malam Abubakar ya samu lambobin yabo da dama daga ciki da wajen Najeriya duba da irin sadaukar da rayuwarsa da ya yi.
Daya daga cikin lambobin yabon da ya samu har daga 'International Religious Freedom Award' da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ba shi a 2019.
An sanar da cewa za a yi jana’izarsa a yau Juma’a 16 ga watan Janairun 2026 bayan sallar Juma’a a kauyen Nghar da ke Jihar Plateau.
Al'ummar yankin da dama sun nuna jimami kan rashin malamin duba da irin gudunmawar da ya bayar a yankin har da Kiristoci.
Yan bindiga sun hallaka malamin Musulunci
Mun ba ku labarin cewa yan bindiga sun hallaka malamin addinin Musulunci a Birnin Gwari da ke jihar Kaduna yayin da yake tattara itacen girki.
Marigayin Malam Bello Abubakar ya rasa ransa ne duk da yarjejeniyoyin zaman lafiya da yan bindiga da aka sanar.
Malamin ya kasance jagoran tafsirin Alƙur’ani a wani masallacin JIBWIS na Juma’a, lamarin da ya girgiza al’ummar yankin.
Asali: Legit.ng

