Babbar Magana: An Gano Yadda Miliyoyi Suka Yi Batan Dabo a Mulkin Yahaya Bello
- Shaida a kotu ta bayyana yadda Hukumar Haraji ta Jihar Kogi ta rika tura makudan kudi zuwa wani kamfani mai zaman kansa a zamanin Yahaya Bello
- Shaidu sun ce an canja ma'ajiyar kudade sama da miliyan 57 zuwa 242 daga KSIRS zuwa wani kamfani daban
- EFCC na tuhumar tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, da karkatar da fiye da ₦110bn, duk da cewa shi da sauran wadanda ake tuhuma sun musanta zargin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wani jami’in banki ya shaida wa Babbar Kotun Abuja yadda wani kamfani mai zaman kansa ya karɓi manyan kudade daga Hukumar Haraji ta Jihar Kogi.
Shaidan, David Ajoma, jami’i a Sterling Bank, ya tabbatar da canja ma'ajiyar kudi guda shida daga KSIRS zuwa 'Bespoque Business Solutions Limited'.

Source: Twitter
An gano batan miliyoyi a mulkin Yahaya Bello
Ya ce wadannan kudade sun kai miliyoyi, kuma an tura su ne a lokacin da Yahaya Bello ke rike da mukamin gwamnan Jihar Kogi, cewar Premium Times.
EFCC na gurfanar da Yahaya Bello tare da Umar Shuaibu Oricha da Abdulsalami Hudu kan zargin karkatar da kudaden gwamnatin jihar.
Hukumar ta ce Bello ya yi amfani da kudaden da ake zargi ya sace wajen sayen gidaje a manyan wurare a Abuja da kuma wani gida a Dubai.
Dukkan wadanda ake tuhuma sun musanta zargin, suna mai cewa ba su aikata laifin karkatar da kudin jama’a ba.
A gaban kotu, lauyan EFCC, Kemi Pinheiro SAN, ya gabatar da bayanan kudaden da aka dauka a matsayin masu matukar tayar da hankali.
Shaidar ta ce a ranar 5 ga Maris 2019, KSIRS ta tura sama da ₦57.9m zuwa asusun BBSL.
Haka kuma, a ranar 4 ga Afrilu 2019, an tura sama da ₦138m da bayanin “Kudin hukumar Kogi na watan Maris.”

Kara karanta wannan
Bayan kashe mutane fiye da 40, Gwamna Bago ya fadi dalilin 'yan bindiga na farmakar Kasuwan Daji
An kuma tura ₦126.8m a ranar 3 ga Mayu 2019, sai ₦97m a ranar 6 ga Yuni 2019, in ji shaidar.
A watan Agustan 2019, BBSL ta karɓi ₦183.6m domin biyan ‘yan kwangila, sannan ₦242.2m domin sayen OPBEH.
Bayan kammala shaidar, alkalin kotu ya dage sauraron shari’ar zuwa 16 ga Janairu domin ci gaba da sauraro.
Wani shaida daban ya ce ma’amalolin da aka yi daga KSIRS zuwa BBSL ba su da cikakken bayani kan manufarsu.
Shaidan ya kuma bayyana cewa sunan Yahaya Bello bai bayyana a matsayin wanda ya amfana kai tsaye daga wadannan kudade ba.
Sai dai ya ce sunan Abdulsalami Hudu ya bayyana sau da dama, inda aka bayyana shi ga banki a matsayin akawun jihar.
A wani bangare, EFCC ta gabatar da bayanan asusun wasu kamfanoni da mutane, inda aka nuna tura kudade zuwa makarantu da kamfanoni daban-daban.
Wasu shaidu sun ce an rika cire kudade da sunan “kudaden tsaro na musamman” daga asusun gwamnatin Jihar Kogi akai-akai.
Kotun ta ci gaba da sauraron shari’ar, yayin da ake sa ran karin bayani zai fito kan mutanen da kamfanonin da abin ya shafa.
Asali: Legit.ng
