Rashin Tsaro: Daruruwan Malaman Musulunci Sun Sauke Alkur’ani, Addu’o’i a Kano

Rashin Tsaro: Daruruwan Malaman Musulunci Sun Sauke Alkur’ani, Addu’o’i a Kano

  • Limaman Najeriya sun fara taron addu’o’i a Kano domin neman taimakon Allah kan tabarbarewar tsaro da matsalolin siyasa da ke addabar ƙasar
  • Taron ya haɗa limamai, shugabannin addini da dubban mabiya, inda aka yi saukar Alƙur’ani da addu’o’in neman zaman lafiya da kariya a ranar Alhamis
  • Ƙungiyar ta ce za a faɗaɗa taron addu’ar zuwa dukkan jihohi 36, tana kiran ’yan Najeriya su haɗa kai wajen roƙon Allah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Ƙungiyar Limaman Najeriya ta gudanar da taron addu’o’i a Kano domin roƙon Allah ya kawo ƙarshen matsalar tsaro da ake fama da shi a kasar.

Malaman sun kuma sauke Alkur'ani mai girma domin kawo karshen rikice-rikicen da ke damun ƙasar nan wanda ke jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

Limamai sun yi addu'o'i a Kano
Dandazon limamai yayin addu'o'i a Kano. Hoto: Ibrahim Sani.
Source: Facebook

An yi addu'o'i a Kano kan rashin tsaro

Kara karanta wannan

Zafin siyasa bai hana aiki: Abba ya fadi shirin gwamnati a kan matasa 50, 000 a Kano

An gudanar da taron a Masallacin Sheikh Ahmadu Tijjani, inda limamai da mabiya daga sassa daban-daban suka taru domin yin addu’a kan ƙalubalen tsaro da siyasa, cewar Aminiya.

Shugaban ƙungiyar, Sheikh Muhammad Nasir Adam ya koka game da halin da ake ciki a kasar musamman a yankin Arewacin Najeriya.

Shehin Malamin ya ce sun shirya taron addu'o'in ne bayan kungiyar ta yanke shawarar daukar matakin domin neman taimakon Allah musamman kan matsalar tsaro.

Shugaban ƙungiyar, Sheikh Muhammad Nasir Adam, ya ce:

“Mun taru a nan bisa shawarar ƙungiyarmu… domin neman taimakon Allah kan matsalar tsaro.”
Malamai sun yi addu'o'i a Kano kan ta'addanci
Taswirar jihar Kano da ke fama da hare-haren yan bindiga a wasu yankuna. Hoto: Legit.
Source: Original

Matsalolin da Najeriya ke fama da su

Sheikh Muhammad Nasir Adam ya bayyana cewa Najeriya na fama da Boko Haram, ’yan bindiga da masu garkuwa, yana mai cewa addu’a ita ce babban makamin al’umma a halin yanzu.

“Mun fahimci cewa addu’a ita ce zaɓi na ƙarshe kuma ita ce babbar makaminmu, da roƙon Allah ya kare ƙasar."

- Sheikh Nasir

Limamin ya ce Najeriya ƙasa ce mai albarka da mutane masu juriya, yana kira ga haɗin kai, tawali’u da yawan addu’a domin samar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Akwai tagomashi: Najeriya ta kulla sabuwar yarjejeniya da Daular Larabawa

Ƙungiyar malaman ta buɗe ƙofa ga dukkan ’yan Najeriya, ba tare da la’akari da addini ko aƙida ba, su shiga wannan aiki na addu’a.

Ta kuma sanar da cewa taron da aka fara a Kano zai ci gaba da gudana a dukkan jihohi 36 na Najeriya domin neman taimakon Allah game da fama da rashin tsaro.

Kano: Malamai sun yi addu'o'i ga Tinubu, Barau

A wani labarin, kungiyar wasu limamai a jihar Kano ta shirya addu’o’i na musamman domin samun nasarar shugaban kasa, Bola Tinubu da Sanata Barau Jibrin.

Kungiyar ta kunshi malaman Musulunci inda suka yi karatun Alkur'ani mai girma saboda samun nasara a zaben 2027 mai zuwa.

Malaman sun yi addu'o'i ga Tinubu da Barau, suna roƙon zaman lafiya, cigaban tattalin arziki, da kwanciyar hankali a ƙasar baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.