Batun Tsaro: Sojojin Najeriya da Amurka Sun Hadu a Abuja
- Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya ya nemi a zurfafa haɗin gwiwar dabaru tsakanin sojojin Najeriya da na Amurka domin tinkarar ƙalubalen tsaro
- Ziyarar jakadiyar tsaron Amurka ta buɗe tattaunawa kan sababbin hanyoyin haɗin kai da za su ƙara wa sojojin Najeriya ƙwarewa da inganci a yaki da suke
- Bangarorin biyu sun nuna aniyar faɗaɗa ayyukan haɗin gwiwa a fannin tsaro, musamman wajen tallafa wa jin daɗin dakarun ta ke yaki da 'yan ta'adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya yi kira da a ƙara zurfafa haɗin gwiwar dabaru tsakanin Rundunar Sojin Kasan Najeriya da ta Amurka domin fuskantar matsalolin tsaro.
Ya bayyana hakan ne a ranar 14, Janairu, 2026, lokacin da Jakadiyar Tsaron Amurka a Najeriya, Laftanar Kanal Semira Moore, ta kai masa ziyarar girmamawa a hedikwatar sojin kasa da ke Abuja.

Source: Facebook
Rundunar sojin Najeriya ta wallafa a Facebook cewa taron ya mayar da hankali kan irin rawar da haɗin gwiwar ƙasashen waje ke takawa wajen ƙarfafa tsarin tsaron cikin gida da kuma tabbatar da dorewar zaman lafiya.
Alakar soji tsakanin Najeriya da Amurka
Laftanar Janar Waidi Shaibu ya bayyana cewa sauye-sauyen yanayin tsaro a Najeriya na buƙatar ƙarin haɗin kai da ƙasashen da ke da gogewa a fannin soja.
Ya ce Rundunar Sojin Kasa na Najeriya na buƙatar amfani da dabaru na zamani da ƙwarewar da sojojin Amurka suka tara tsawon lokaci, domin magance barazanar tsaro ta hanyoyi daban-daban.
A cewarsa, ƙarfafa irin wannan haɗin gwiwa za ta taimaka wajen inganta kwarewar aiki, tsara dokoki da dabaru, da kuma ƙarfafa ƙarfin rundunar a matakin dabarun kasa.
Najeriya ta gode wa kasar Amurka
The Cable ta rahoto cewa Babban Hafsan ya yaba wa gwamnatin Amurka bisa ci gaba da goyon bayan da take bai wa sojojin Najeriya tsawon shekaru.
Ya bayyana cewa rundunar ta amfana sosai daga kwarewa da tsarin horon sojojin Amurka, inda ya nuna cewa shi da wasu manyan jami’an rundunar sun samu horo a fitattun cibiyoyin soji na Amurka.
Waidi Shuaibu ya ce wannan alaka ta horo da musayar kwarewa na nuna zurfin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, tare da tasirin da take da shi wajen gina rundunar soji mai inganci.
Matsayar Amurka kan alaka da Najeriya
A nata bangaren, Laftanar Kanal Semira Moore ta nuna godiya kan kyakkyawar alaƙa da ke tsakanin sojojin Najeriya da na Amurka.
Ta jaddada aniyar ƙasarta ta ci gaba da ƙarfafa dangantakar da ke akwai tare da buɗe sabbin hanyoyin haɗin kai, musamman a fannonin samar da ƙwarewa, musayar bayanan sirri da kuma tsara ayyukan hadin gwiwa.

Source: Facebook
Bayani kan harin Amurka a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi bayani game da harin da Amurka ta kawo Sokoto a ranar 25 da Disamban 2025.
Kakakin 'yan sanda na kasa, Benjamin Hundeyin ya bayyana cewa suna da wasu bayanai game da abubuwan da suka faru yayin harin.
Sai dai duk da haka, Hundeyin ya ce 'yan sanda ba za su fito su yi magana game da harin ba, za su bar dakarun tsaro na soji su yi bayani.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

