Christopher Musa Ya Bayyana Abin da Ke Rura Wutar Rashin Tsaro a Najeriya
- Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya samo mafita kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
- Janar Christopher Musa ya bayyana cewa akwai matsalolin da ke rura wutar matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
- Ministan tsaron ya bukaci al'ummomin da ke bakin iyakokin kasar nan da su guji tallafawa ayyukan 'yan ta'adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.
Christopher Musa ya ce iyakokin kasar nan da ba su da cikakken tsaro na kara rura wutar matsalar rashin tsaro da Najeriya ke fuskanta.

Source: Twitter
Ministan tsaron na Najeriya ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar BBC Pidgin ta yi da shi.

Kara karanta wannan
'Dabarar da sojoji ke yi wurin kubutar da mutane daga ƴan bindiga': Ministan tsaro
Gwamnati na kokarin samar da tsaro
Christopher Musa ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na duba hanyoyi daban-daban, ciki har da gina katanga a kan iyakoki da amfani da fasahohin zamani.
Ya ce za ta bi hanyoyin ne domin hana ketare iyaka ba bisa ka’ida ba, wanda ke bai wa ’yan ta’adda, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane damar yin barna a fadin kasar nan.
Me ke rura wutar rashin tsaro?
“Iyakoki marasa tsaro na daga cikin manyan dalilan rashin tsaro a Najeriya."
- Christopher Musa
Ya ce duk da cewa gina katanga a dukkan fiye da kilomita 4,000 na iyakokin kasar nan na kasa ba abu ne mai sauƙi ba, fasaha na iya taimakawa wajen sanya ido kan zirga-zirga da kuma ankarar da jami'ai idan aka ketare iyaka ba bisa ka’ida ba.
Tsohon hafsan tsaron na kasa ya kara da cewa wasu kasashe ma da ke da iyakoki mafi tsawo sun aiwatar da irin waɗannan matakai cikin nasara.

Kara karanta wannan
"Abokin barawo": Ministan tsaro ya gargadi Sheikh Gumi da masu goyon bayan 'yan ta'adda
Gwamnati za ta hada kai da al'ummomi
Christopher Musa ya ce gwamnati na shirin yin aiki tare da al’ummomin da ke kusa da iyakoki domin su fahimci rawar da suke takawa wajen dakile ayyukan ’yan ta’adda.

Source: Facebook
“Wataƙila ba za mu iya gina katanga a ko’ina ba, amma akwai fasahar da za mu iya amfani da ita cikin tsari. Da zarar wani ya ketare iyaka, za a gani, sannan mu ɗauki mataki."
“Muna buƙatar wayar da kai da kuma tattaunawa da al’ummomi domin kada su tallafa wa ’yan ta’adda ta kowace hanya.”
- Christopher Musa
Ministan tsaro ya gargadi Sheikh Gumi
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya aika da sakon gargadi ga Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi.
Christopher Musa ya yi gargadin ne ga Sheikh Gumi gargaɗi ga Sheikh Ahmed Gumi da sauran mutanen da ke nuna goyon baya ko tausayawa ‘yan ta’adda da ‘yan fashi da makami.
Ministan tsaron ya bayyana cewa abokin ɓarawo shi ma ɓarawo ne, inda ya ce wajibi ne a daina mara wa masu aikata laifuffuka baya.
Asali: Legit.ng