'Yan Bindiga Sun Mamayi Mutane, Sun Tafka Barna a Babbar Kasuwa a Jihar Zamfara

'Yan Bindiga Sun Mamayi Mutane, Sun Tafka Barna a Babbar Kasuwa a Jihar Zamfara

  • 'Yan bindiga dauke da mugayen makamai sun kai farmaki babbar kasuwar dabbobi a karamar hukumar Kaura Namoda, jihar Zamfara
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun kwace tare da yin awon gaba da shanu fiye da 500 a harin, amma an yi nasarar dawo da 60
  • Shugaban kungiyar makiyaya (MACBAN) reshen jihar Zamfara, Aminu Garba ya ce wannan ba shi ne karo na farko da 'yan bindiga suka farmake su ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Wasu ’yan bindiga dauke da manyan makamai sun kwace shanu sama da 500 a Kasuwar Daji da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara.

Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Ƙasa (MACBAN) reshen Zamfara, Kwamared Aminu Garba, ya bayyana cewa wannan ba shi ne karo na farko da aka samu irin wannan hari ba.

Kara karanta wannan

Cikin rashin imani, 'yan bindiga sun harbe 'matar sarki' mai shekara 75

Jihar Zamfara.
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya bayyana cewa makamancin haka ta faru kusan shekaru huɗu da suka gabata a wannan babbar kasuwa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

“Ba wanda ya yi tsammanin hakan zai sake faruwa, amma mun taɓa fuskantar irin wannan mummunan lamari kusan shekaru huɗu da suka wuce,” in ji Aminu Garba.

Yan bindiga sun shiga kasuwar Daji

Ya ƙara da cewa ana zargin ’yan bindigar sun shigo kasuwar da ƙauyukan da ke kewaye da ita tun da rana, inda suka rika bibiyar harkokin saye da sayar da dabbobi tare da lura da masu saye.

A cewarsa, yawancin shanun da maharan suka kwace an sayo su ne daga kasuwanni daban-daban, ciki har da wasu da aka shigo da su daga Jamhuriyar Nijar, aka ajiye su a Kasuwar Daji kasancewarta babbar kasuwar dabbobi a yankin.

“Yawanci muna fara sayen dabbobi ne tun ranar Laraba har zuwa ranar kasuwar Daji kafin a ɗora su a manyan motoci zuwa Legas,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wani abu da ake zargin bam ne ya tarwatse da mutane a Adamawa

Yadda maharan suka sace shanu 500

Ya ce ’yan bindigar sun kwashe shanun ne da dare, inda suka tsere ta ɓangaren yammacin ƙauyen Kasuwar Daji.

“Sun fi mutane 50, kuma suna dauke da manyan makamai. Sun yi aikin da dare, sannan suka nufi yammacin kasuwar saboda hanyar tana kaiwa kai tsaye zuwa daji,” in ji Aminu.

Sai dai ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya shafa, Alhaji Sani Yaba Ajiyan Fawa, ya ce adadin ’yan bindigar ya haura 100, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Gwamna Dauda Lawal.
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal lokacin kaddamar da askarawa domin yaki da yan bindiga Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Ya bayyana cewa shanun da aka kwace mallakin masu kiwo ne da ake kira ‘Yantugu’ a harshen Hausa, inda ya ƙara da cewa kusan shanu 60 ne aka samu nasarar dawo da su.

“Kamar yadda kuka sani, yana da matuƙar wahala a sarrafa manyan dabbobi a irin wannan rikici. Waɗanda aka dawo da su, su ne waɗanda suka watse a lokacin harin,” in ji shi.

Sojoji sun yiwa yan bindiga lugude a Zamfara

Kara karanta wannan

Yaran Turji sun yi ta'asa a Sokoto bayan sakon dan ta'addan ya rikita jama'a

A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojojin sama ta Najeriya (NAF) karkashin Operation Fansa Yamma, ta ragargaji 'yan ta'adda a jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin saman sun samu nasarar kashe 'yan ta'adda da dama bayan sun farmake su a karamar hukumar Tsafe.

Rundunar sojin ta gudanar da hare-haren sama guda biyu masu tsananin tasiri a Dutsen Turba da kuma sansanin Kachalla Dogo Sule.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262