Tashin Hankali: Matar Aure Ta Yi Amfani da Adda, Ta Kashe Mijinta da Budurwarsa
- Wata matar aure a jihar Delta ta kashe mijinta da budurwarsa bayan ta yi amfani da adda da guduma wajen fasa masu kai
- Rundunar yan sanda ta kama matar bayan ta raunata makwabciyarta wadda ta yi kokarin shiga tsakani domin ceton ran mijin
- A jihar Ondo ma wata matar ta fasa wa mijinta kai da tabarya sakamakon zargin cin amana wanda hakan ya janyo mutuwarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Delta - Wani mummunan lamari ya girgiza yankin Ighwre-Ovie da ke ƙaramar hukumar Ughelli ta Arewa a Jihar Delta, bayan wata mata ta kashe mijinta da adda.
An ce matar auren, wacce ’yar asalin kabilar Isoko ce, ta hallaka mijinta da wata matar da take zargin budurwarsa saboda tsabar kishi.

Source: Twitter
Wata mata ta kashe mijinta da adda
Matar, wadda uwa ce ga yara biyu, yanzu haka tana hannun hukuma a hedikwatar rundunar ’yan sanda ta Ughelli, in ji rahoton Vanguard.
Rahotanni sun nuna cewa matar ta daɗe tana zargin mijinta da cin amanarta da wata matar, amma ubangiji bai ba ta damar yin wani abu a kai ba.
Amma a ranar da ta hau dokin zuciya, mijin ya dawo gida cikin maye, inda ta yi masa maraba da sara da adda a kansa, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa nan take.
Matar ta kashe budurwar mijinta
Bayan ta kashe mijin nata, matar ba ta tsaya a nan ba; wata maƙwabciyarta da ta yi ƙoƙarin shiga tsakani domin kwatar mijin, ta samu munanan raunuka a haɓarta sakamakon saran adda, inda yanzu haka take kwance a asibiti.
Daga nan, matar ta nufi gidan matar da take zargin budurwar mijin nata ce, wadda ke zaune a kusa da su, cewar rahoton Linda Ikeji.
Bayan ta shiga gidan matar, ta yi amfani da guduma ta fasa mata kai, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarta.
Wata mata da ta ji hayaniya ta yi maza ta fito ta yi kururuwa, wanda hakan ya sa mutane suka taru aka yi nasarar kama wadda ake zargin.

Source: Original
Makamancin wannan lamari a Ondo
Wannan rashin imani na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu labarin wani kusan makamancin hakan a garin Akungba, Jihar Ondo, in ji rahoton The Sun.
A can ma, wata matar aure mai suna Omolara Oluwakemi, ana zarginta da amfani da taɓarya ta fasa wa mijinta, Seidu Jamiu, kai yayin da yake barci.
An bayyana cewa ma'auratan sun yi cacar baki a daren ranar kan zargin rashin amana kafin matar ta aikata wannan danyen aiki. Kodayake rundunar ’yan sandan Jihar Delta ba ta riga ta fitar da sanarwa ta hukuma ba, wani babban jami’in tsaro ya tabbatar da cewa wadda ake zargin tana hannunsu kuma ana ci gaba da bincike mai zurfi.
Amarya ta kashe angonta a Kano
A wani labari, mun ruwaito cewa, an samu tashin hankali a Kano yayin da wata amarya, Saudat Jibrin ta daba wa angonta Salisu Ibrahim wuka har lahira.
Rahotanni sun bayyana cewa an daura auren Saudat da Salisu a ranar 27 ga Afrilu, kuma amaryar ta kashe angonta a darensu na tara.
Wani ganau ya ce Saudat ta yanka Salisu a wuya bayan ta nemi ya rufe idonsa da sunan za su yi wasa, kuma ya mutu bayan an kai shi asibiti.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


